Advertising
Advertising
Uncategory

Mansura Isa ta fadi dalilin dayasa ta saka sani danja a Film dinta na fanan bayan rabuwar su.

Tsohuwar jaruma a masana’antar kannywood Mansura Imam, wadda akafi sani da Mansura isa tsohuwar matar Sani danja. ta fadi dalilin dayasa tasa tsohon mijin ta a Film dinta mai suna “FANAN“.

Advertising

Kaman yadda kuka sani dai Mansura Isa ta kasance tsohuwar jaruma a Kannywood wadda tayi shuhura kuma tauraran ta ya haska dai dai gwargwado.

Dayawa mutane basu san jarumar tana daukar nauyin fina finai ba ma’ana Furodusa ce ita tun kafin tai aure. haka kuma itace shugaban Today’s Life Foundation.

Jaruma dai ta shirya wani Gagarumin Film wanda a yanzu haka sunan sa da wakokin ciki suka karade wayoyin al’umma wato “FANAN“.

Advertising

Mamallakiyar Film din Mansura Isa ta tattauna da mujallar Hausa Film akan Film din Fanan, inda mujallar tayiwa jarumar tambaya akan yadda akai gabin tsohon mijin ta a cikin Film din.

jarumar ta bada amsa kaman haka:

Mun fara daukar Film din tun a shekarar data gabata ma’ana shekara 2020, Disamba zuwa Fabrairu muka kammala daukar kowane bangare na Film din, Amma wakoki ne suka rage mana wadda bamu dauka ba, Saka makon a lokacin ana fama da COVID-19. da bamu samu lokaci ba sai muka barshi sai kwanan muka kammala amma ba yanzu mukai Film din a cewar Jarumar.

Mungode da ziyartar shafin mu, ku cigaba da kasancewa damu domin samu labarin masu inganci.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button