Labaran Kannywood

Za’a yi wa jarumi Hamza Yahaya aiki a hancin sa, yana neman taimakon al’umma.

Allahu Akbar jarumi Hamza Yahaya yana cikin wani hali akan ciwon da wasu yan bindiga suka ji masa a lokacin da suke kan hanya ta zuwa jihar Kano daga garin Legas.

Idan baku manta ba a yan kwanakin baya da suka wuce mun baku labarin yanda akai wa Hamza Yahaya aiki akan hancin nasa, inda muka nuna muku hotunan yanda Allah Ya mai da shi bayan anyi aikin.

Hakika labarin Hamza Yahaya, labari ne mai cike da ban tausayi, inda wasu ma har sukan zubar da hawaye idan kukaji abinda ya faru da shi.

Hamza Yahaya dai ya hadu da ibtila’a ne na yan bindiga shi da abokin sa mai suna Ataka, inda yan bindigar suka bude musu wuta, lamarin da yasa harsashi ya wuce ta gefen hanzin Hamza wanda ya haddasa mai mummunan rauni akan hancin.

Inda shi kuma Ataka wato abokin tafiyar Hamza harsashi ya same shi a cinya inda shima ya haddasa mai mumman rauni, sai dai babu wanda ya rasa ran sa a cikin su.

Kuma duk wannan abu mara dadi ya faru da su ne a lokacin da suke kan hanyar zuwa Kano daga garin Legas.

To a halin yanzu dai duk da cewa anyi wa Hamza aiki akan hancin sa amma har yanzu da sauran tsalle inji Hausawa domin kuwa baya iya numfashi da hancin sosai, sai dai ta baki dalilin da yasa baya iya samun bacci.

Hakane kuma yasa ake neman taimakon al’umma domin ana su a hada kudi a sake yi masa aiki na musamman akan hancin, domin a ceto rayuwar sa. Bari kuma kuji karin bayani daga bakin Mustafa Naburaska akan wannan al’amari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button