Labaran Kannywood

Sanata Barau ya dau nauyin Jarumi Hamza Yahaya kasar waje domin yimasa aiki.

Idan baku manta ba a yan kwanakin baya da suka wuce mun baku labarin yanda akai wa Jarumi Hamza Yahaya aiki akan hancin nasa, inda muka nuna muku hotunan yanda Allah Ya mai da shi bayan anyi aikin.

Hamza Yahaya dai ya hadu da ibtila’a ne na yan bindiga shi da abokin sa mai suna Ataka, inda yan bindigar suka bude musu wuta, lamarin da yasa harsashi ya wuce ta gefen hanzin Hamza wanda ya haddasa mai mummunan rauni akan hancin.

Bayan an masa aiki ne sai yanzu kuma baya iya numfashi yadda ya kamata, Hakan yasa baya iya bacci ko kadan. Wasu daga cikin jaruman Kannywood sun nemi gwamnati ta temakawa Hamza ai masa aiki a shekaran jiya.

Sai gashi a jiya talata Sanata Barau I Jibril Maliya ya dauki nauyin kai jarumin kannywood hamza kasar waje domin ai masa aiki a hancin nasa.

wannan abu ba karamin dadi yay jaruman Kannywood ba kasancewar sanata ya nuna suna da muhimmanci a garesu.

Zaku iya kallon wannan video dake kasa dan ganin yadda abun da yafaru.

Bayani daga bakin jarumi Ali Nuhu bisa wannan abin Alkhali da Sanata yay musu akan aikin wannan Jarumi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button