Yan bindiga sun halaka wasu masuyin sallaha a masallaci.

Ana zargin wasu yan bindiga da halaka mutun 10 a dai dai lokacin da suke tsaka dayin sallah magriba a jamhuriyar Nijar cikin wani masallaci.
Wasu mahara sun yiwa wani kauye kawanya mai suna Abankor a jamhuriyar Niger, Maharan sunwa kauyen dirar mikiya ne da yammacin ranar laraba akan babura.
Maharan sun kai sumame kauyan akan babura a dai dai lokacin da al’ummar musulmai ke tsaka da gaida mahaliccin su da magariba suka bude masu wuta; a cewar wanda abun ya faru a gaban sa.
Jahar da aka kai harin ta Tillaberi, inda kauyen Abankor yake a Jamhuriyar Nijar na makawabtaka da kasashen Mali da kuma Burkina Faso.
Hare-haren mahara na kara tsamari a yankin tun farkon da muka shiga wannan shekara ta 2021, musamman a yankunan da sukai iyaka da kasashen guda biyu lamari yafi tsamari.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi jan kunne na farkon watan Oktoba cewa mutun 600,000 jihar Tillaberi na fuskantar yinwa wajen ra’a abin da zasu ci.
Source: Aminiya