Allah Akbar’ abin da yafaru da jarumar kannywood Zpreety aka dena jin duriyar ta.
Yadda aka shafe tsawon lokuta ba a jin duriyar Sharariyar jaruma Zulaihat Ibrahim wadda aka ci sani da Zpreety a cikin fina finan Hausa, Hakan ba karamin ce-ce kuce ya jawo ba.
Zulaihat Ibrahim ta kasance mai barkwanci wadda indai tana waje sai an sani, amma sai ya zama an dade ba a jin ta ko ganin ta a cikin kannywood, hatta a shafukan ta na Social media ma ba a ganin ta kwata-kwata.
Zpreety na daya daga cikin jaruman da su ka fi kowa yin bidiyon kan su, su dora a shafin su na Social media.
Labarin daya game kafar sada zumunta tun watan biyar daya gabata na cewar Zpreety ta samu kan ta cikin mawuyacin rashin lafiyar, inda har ta koma garinsu chan jihar Kebbi.
Babban abin da ya kara tabbatar da rashin lafiyar Zpreety shine rashin samun ta a waya da aka denayi, kum duk abokan aikin ta in aka tambaye su labari a game da ita sai su e sudai sunsan bata da lafiya amma ba’a samunta a waya.
Rana daya sai gashi anga post din Zpreety a social media, Hakan ya tabbatar da cewar jarumar ta samu sauki.
Wakilin mu ya jima yana ta gwada wayar ta kullum a kashe. sai a daren Asabar akai sa’a wayar tana kunne.
A gajeriyar hirar da sukai da Zulaihat ta tabbatar wa da wakilin mu cewa lallai ta dade bata da lafiya.
A cewar ta, “tabbas na yi rashin lafiya kuma na kwna biyu a kwance, shi ya sa ma ba na daga waya domin ban san wanda zai kira ni ba, kuma ina cikin wani hali ne a lokacin.
“Amma yanzu alhamdulillah na samu sauki tunda ga shi yanzu mu na yin magana da kai.
“Abubuwa da dama da bana iya yi, yanzu ina yi. Don haka na samu sauƙin jiki na.”
Da Wakilin mu ya tambaye mata maganar rade radin cewa wai an yi mata asiri ne, wanda shi ne dalilin rashin lafiyar tata, sai ta ce, “Ai na zata ka kira ni ne don ka gaishe ni ba don neman labari ba. Don haka in don wannan ne, ka bari nan gaba zan kira ka mu yi maganar.”
Wakilin mu ya tambayeta yaushe zata dawo kano domin dorawa a inda aka tsaya, sai ta ce, “Yanzu dai ina garin mu idan gari yay lafiya zan dawo insha Allah.”