Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Rigima tsakanin mashiryan shiri mai dogon zango a Kannywood.

Wani Abu da ya ke neman zama ruwan dare shine yadda masu shirya shiri mai dogon zango a Kannywood ke yawan saumun sabani da jarumai musamman mata.

Advertising

Hakan na faruwa da masu jagorantar shirin, Wanda irin haka ya faru a fina-finai da dama. mafiya shara sune Bugu Zuciyar Masoya inda a dalilin cire jaruma Hannatu Usman takai ga ta zagi darakta har Lawan Ahmad ya tsinke ta da mari a gurin daukar shiri.

A kwanakin nan ma kun ji yadda dalilin cire Ummi Rahab daga Farin wata sha kallo aka dinga taraliya tsakanin ta da Adam A Zango.

Adam A zango da Ummi Rahab.

Anan ma irin haka ce ta faru tsakanin Jaruma Rahama Kumo, Wacce aka fi sani da Jamila Makira da darakta da producern shirin jamila makira inda labari yafara yawo cewa an cire jarumar daga shirin har tayiwa mashiryan shirin zagin tsamar nama.

Advertising
Masu kamfanin brothers point multimedia da jamila Makira

Rahama Kumo dai in bazaku manta ba ita ce jarumar da kwanakin baya muka kawo muku labarin ta musulunta sanadiyyar film ta kuma sha gwagwarmaya kafin ta samu fitowa a shirin “Jamila makira” na kamfanin brothers point multimedia da ke zuwa a YouTube channel mai suna makira tv.

Lawan Ahmad da Hannatu Usman

Domin jin yadda lamarin ya faru mun tuntubi Rahama kan wannan batu inda ta bayyana mana ita ma yadda ake jita jita haka taji cewa an cire ta a shirin bata da masaniya.

Kawai dai taga an fita location ba tare da an sanar da itaba, kuma alaka ta dan yi sanyi tsakanin ta da masu shirin domin takan yi musu magana basa amsawa dan haka da taji jita-jitan an cireta ta hadda cewa abincin ta ya kare a shirin.

Munji ta bakin Mashiryan Film din inda sukace, aiki za’a fita amma sina sinan da za’a dauka babu ita a ciki nata sai bayan sati daya, kawai sai muryata aka kawo mana tana zage-zage wai an cireta a Film, Su kuma kawai jin haka yasa suka cire ta tunda tace haka.

Allah ya kyautata, kucigaba da bibiyar mu dan samun labarai ingantattu.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button