Jaruman kannywood din da sukaci ribar hakar Film kuma har yanzu ake damawa dasu.
Jaruman kannywood mata wanda a yanzu haka suke shirya fina finai kuma suke kasuwanci. zaku iya ganin jerin wannan jarumai da kuma irin fina finan da suke shiryawa.
(1) Mansurah isah itama tsohuwar jaruma ce ta kuma bada gudumuwa sosai a Masana’antar Kannywood, mansura tabar fitowa a matsayin jaruma ne ta dalilin aure da tayi a shekarar 2007.
Ta kuma auri jarumi sani danja wanda suma suna cikin jerin jarumai da auren su yayi Albarka fiye da shekara goma suna tare kuma Allah ya azurtasu da haihuwar yara hudu.
Mansurah itama fittaciyar mai shirya finafinai ce inda a yanzu haka ta gama aikin fitaccen shirin nan nata da ake jira Mai suna Fanan.
(2) Halima yusuf atete wacce a yanzu wasu ke kiranta da queen of Kannywood, an haifeta a garin maiduguri a shekarar alif 1988.
Ta shigo cikin Masana’antar Kannywood a shekarar 2012 sannan kuma ta fara fitowa acikin film din Asalina, ta kara fitowa a finafinai da dama irin su igiyar zato, bikin yar gata, matar jami’a da kuma film din dakin amarya wanda shine film dinda ya daga tauraron ta.
Jarumar itama ba’a barta a baya ba, domin tana cikin jerin mata da suke shirya Finafinai a Masana’antar Kannywood.
(3) Hannatu Bashir da akafi sani da Hanan, Ta shigo cikin Masana’antar ta Kannywood a shekarar 2012, tana cikin jerin jarumai mata da suka samu daukaka fiye da sauran jarumai wanda sun kwashe shekaru suna gabatar da harkar.
Kusan a yanzu jarumar tafi maida hankali ne ta bangaren shiryawa fiye da fitowar ta acikin finafinai, sannan itama ta shiga cikin harkakar kasuwanci bayan sana’ar film da takeyi.
(4) Fitaccen mai bada umurni watau Hassan giggs, Suna cikin jerin jaruman Kannywood da Suka auri Junan su kuma auren yayi albarka, domin sunkwashe kimanin shekaru 14 suna tare.
Jaruman suna matukar shan yabo a wajen masoyan su kasacewar mafi yawancin Jaruman da suka auri zunan su auren baya dadewa.
Muhibbat itace mace ta farko a Kannywood da take bada umurni a Finafinai kasancewar wannan aiki ne da maza sukafi rinjaye, jarumar ta bayyana cewa tin farkon Shigowar ta cikin Masana’antar take da sha’awar zama mai bada umurni.
Sannan burin ta ya cika ta dalilin mijinta wanda shine yake dorata akan hanya wajen nuna mata yadda ayyukan suke, bayan kuma sana’ar film muhibbat tana kasuwanci na kayan kwaliyya da sauran su.
(5) Rukayya Umar santa da akafi sani da rukayya dawayya daya daga cikin fitattun jarumar Kannywood, an haifeta a jahar kano amma ta girma a kasar saudi arabia ta shigo cikin Masana’antar Kannywood tin a shekarar 2000 sannan tayi fice a acikin film din dawayya.
Wannan film shine lakabin sunan yake binta har izuwa yanzu kuma da wannan suna mutane suka santa, jarumar ta fito acikin finafinai da suka kai akalla guda 100.
Sannan ta taba yin Aure a shekarar 2013 inda Allah ya azurtata da haihuwar yaro daya namiji wanda ake kira da Arafat.
Rukayya tana cikin jerin matan Kannywood da suke shirya finafinan a karkashin kamfanin ta mai suna dawayya Movies nigeri limited.
Acikin jerin finafinan da jarumar ta shirya sun hada da Hajjaju, kunyi sake, Halimatus sadiya, Nawwara da kuma ummi sambo da sauran su, daga karshe jarumar bayan harkar film da takeyi itama tana taba kasuwanci.
(6) Rashida Adamu Abdullahi da Akafi sani da Rashida mai sa’a itama dai tsohuwar jarumar kannywood ce sannan kuma babbar yar kasuwa, tana daya daga cikin manyan jaruman Kannywood mata, ta dade tana shirya finafinai a karkashin kampanin ta me suna Mai sa’a international limited.
Cikin jerin finafinai data shirya a kampaninta sun hada da film din Sa’a, labarin duniya, fadi alkhairi, da kuma khadijatu ko aisha da sauran su.
Jaruma ta biyar sannan kuma ta karshe acikin jerulin matan Kannywood da suke shirya finafinai itace
Kusan a yanzu jarumar tafi maida hankali ne ta bangaren shiryawa fiye da fitowar ta acikin finafinai, sannan itama ta shiga cikin harkakar kasuwanci bayan sana’ar film da takeyi.