Advertising
Advertising
Labarai

Yan Sanda sun cafke mai kaiwa yan bindiga makamai da abinci.

Hukumar yan sandan jihar kano tayi nasarar kame mutumin da yake kaiwa yan bindiga makamai da kuma fetur a karamar hukumar Fage.

Advertising

Mai magana da yawun yan Sanda jihar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan, inda yace sun kama mutanan biyu a wata mota kirar J5 a makare da abinci da kuma man fetur.

Mutumin da ake zargin dan shekara 31 a duniya dayan kuma dan shekara 37 dunkan su yan asalin jihar Katsina ne.

Kiyawa ya ce, Ranar 15/10/2021 da midalin karfe 12:30 na rana jami’an yan Sanda karkashin CSP Abubakar Hamma sukai nasarar damke motar kirar J5 dare da wasu mutane biyu dauke da kayan abinci.

Advertising

A dai dai lokacin da ake duba motar an gano jarkar man fetur 25 guda biya cike da man fetur, wanda ko wace jarka an sakata cikin buhun sukari domin badda kamar ta.

Mutun daya da ake zargi yace ya fito ne daga chan garin jibiya a jihar Katsina, yazo nan kano ne domin ya siya fetur ya kaishi chan inda zai siyar da mugun tsada.

Mutumin da ake zargin yace wannan shine karo na biyu ana kamashi yana safarar man fetur, kaka kin ya ce, aje a zurfafa bincike akansu domin tabbatar da gaskiya daga nan kuma a makasu a kotu.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button