Yadda wani matashi mai suna Aliyu Idris yayi yunkurin sayar da kansa Naira Miliyan 20M dalilin bai sami ganin Naziru Sarkin Waka ba
Matashin da yayi yunkurin sayar da kansa ya bayyana cewa: Rashin ganin Mawaki Naziru M Ahmad ne ya jefa shi cikin wannan halin, sannan kuma matashin yace shi ba dan Kano bane yazo ne da ga Kaduna domin yaga mawaki Nazir M Ahmad, amma bai sami damar ganin sa ba har tsawon kwanaki biyar 5 sabida haka ya yanke shawarar sayar da kan sa.
Matashin mai suna Aliyu Idris ya bayyana, yazo ne daga Tudun wada dake jihar Kaduna musawa round about taka lafiya road, inda kuma yace shi tela ne.
Aliyu Idris ya kara da cewa, yana sana’anr dinkin tela ne sannan kuma yana rera waka domin kuwa ya taba rerawa Nazir M Ahmad wakoki biyu daya wanda yaji labarin Naziru sarkin waka zai je jihar Kaduna.
Matashin Aliyu Idris ya kara da cewa, Ya sami wadanda zasu saye shi kimanin Naira Miliyan goma sha biyar 15M, inda shi kuma ya sanya farashin kan sa a Naira Miliyan ashirin 20M.
Ga cikekkiyar bidiyon nan domin ku kalla kuji sauran bayani daga bakin matashin Aliyu Idris kan yadda yaje son mawaki Nazir M Ahmad wanda kuka fi sani da Sarkin waka.