Labaran Kannywood

An gano cewa jarumi Adam a zango da Rahama Sadau sunfi janyowa kannywood zagi da cece-kuce

A wani bincike da masana suka gudanar sun tabbatar da cewa jarumi Adam a zango da Rahama Sadau sun fi kowa janyowa masana’antar kannywood zagi da cece-kuce.

Kamar yadda kuka sani kannywood masana’anta ce wacce ake shirya fina-finan tare da rera wakoki kala kala, sannan kuna masana’antar tana da tarin masoya da dama wanda har kullum karuwa suke.

Tun lokacin da aka kafa masana’antar kannyood ba’a taba yin wani al’amari wanda ya tada kura ba sannan kuma yayi ta yawo a kafafan sada zumunta kuma duniya ta helanta shi, kamar yadda wani al’amari da yafaru da wata tsohuwar jaruma wanda ta dade da dai na harkar fim gaba daya wato, Maryam Hiyana.

Sannan kuma tun bayan cece-kucen da akayi akan tsohuwar jaruma Maryam Hiyana ba’a taba samin wani cece-kuce wanda ya hargitsa masana’antar kannywoid ba sama dana jaruma Rahama Sadau.

Wanda hakan yasa masu bincike akan harkar fina-finai ta kannywood suka tabbatar da cewa, babu jarumar da aka fi tattaunawa a kanta sama da Rahama Sadau da kuma Adam a zango.

Cece-kucen da Rahama Sadau ta fara janyowa a kannywood din shine lokacin da jarumar tayi waka da wani mawakin gambara na Hip Hop mai suna Buba Barnabas wanda kowa yafi sanin sa da Classiq, inda a cikin bidiyon wakar aka ga jaruma Rahama Sadau ta rungomeshi al’amarin daya tayar da hankulan jama’a duba da yadda ba’a saba ganin irin wannan halayyar a masana’antar kannywood wanda har aka koreta daga kannywood din.

Hakan yasa wani mawakin turanci dan kasar Amerika mai suna Akon ya kira Rahama Sadau domin ya taimaka mata dalilin korar ta da aka yi daga kannywood, a wannan lokacin jama’a da dama basu san jaruma Rahama Sadau ba sai bayan hotunan su sun bayyana tare da wannan mawakin mai suna Akon dan kasar Amerika.

Bayan bayyanar hotunan nasu sai jama’a suka fara tunani na daban akan jaruma Rahama Sadau inda wasu ke fadin cewa ta koma kasar Amerima komai ma zai iya faruwa, wasu kuma suke fadin cewa ai hakan babbar nasara ce ga rayuwar domin zata sami daukaka matuka.

Jarumi Adam a zango.

Idan baku manta ba a kwankin baya da suka shude an taba zan jarumi Adam a zango da neman maza, al’amarin daya janyo cece-kuce da tada kura a masana’antar kannywood dama wajan ta.

Sannan kuma a kwai wani shirin fim wanda Adam a zango ya shirya mai suna saban Sarki, inda yake neman mata masu kananan shekaru wanda hakan ya janyo wani malami yayi masa mummunar fashimta.

Bayan faruwa al’amarin sai jama’a suka maidawa da malamin martani kan cewa wani shirin fim za’a dauka mai dogon zango, wanda fim din da za’a shirya yafi bukatar irin wadannan matan domin su ake bukata a ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button