Advertising
Advertising
Labarai

Sheikh Aminu Daurawa sun kirkiri wata manhaja a waya domin kulla auratayya tsakanin Maza da Mata sabida zaurawa da ‘yan mata sunyi yawa

A wannan zamani da muke ciki akan sami yawan matsala takin aurar zaurawa wanda ‘yan mata ma ba sosai ake aurar rasu ba, duba da yadda zamani ya sanja wanda tsadar rayuwa ta turo kai cikin al’umma amma duk da hakan ba’a fasa ba anayi amma ba kamar baya ba.

Advertising

Kamar yadda kuka sani sha’anin aure ba karamin abu bane wanda mutum zai yi wasa a kansa ba, idan mutum zai yi aure ya kamata ya tsaya ya nutsu wajan zabawa ‘yayan sa uwa ta gani wanda zata basu tarbiyya mai kyau da duniya zatayi alfahari dasu koda bayan rasuwar mahaifan.

Domin rashin samin mace ta gari a zamantakewar aure shike kawo rashin zaman lafiya da gurbacewar tarbiyyar yara, domin ‘yayan ku zasu taso babu nutsuwa babu tarbiyya sannan ta dalilin haka akan sami karancin rashin ilimi a tattare da yaran.

Sheikh Malam Aminu Daurawa babban malamin addini ne na Musulinci wanda ya jagoranci bude wata manhaja ta wayar salular zamani wanda ake amfani da ita a yanzu, wanda duk wani matashi ko matashiya sunfi rike irin wadannan wayoyin wato Android, inda zaka iya samin matar da zaka aure ta dalilin amfani da wannan manhajar dake cikin wayar.

Advertising

Malam Aminu Daurawa yayi cikekken bayami akan wannan manhajar duba da yadda ‘yan mata da zaurawa sukayi yawa a garuruwa, shi yasa suka bullo da wannan hanya tayin amfani da manhajar domin samin yawan auratayya a cikin wannan manhajar.

Sheikh Aminu Daurawa yayi bayani wanda kowa zai gamsu da bayanin nasa a cikin bidiyon da zaku kalla a kasa, sannan kuma idan ka kalli wannan bidiyon zaka karu da abubuwan da baka sani ba wanda zasu amfaneka sosai a rayuwar ka.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

https://youtu.be/HZfuU7YUKlY

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button