Wata bidiyon jarumi Adam a zango da yarinyar sa Tumba Bukar tana shafa shi ta janyo musu cece-kuce
Kamar yadda kuka sani Tumba Bukar ta kasance yarinya ga jarumi Adam a zango wanda tun farko shine yayi silar daukakar ta a masana’antar ta kannywood, a cikin wani fim mai suna Gwaska wanda a kwanakin baya yayi tashe sosai.
Duk da Tumba Bukar ta kasance yarinya ga jarumi Adam a zango hakan ba yana nufin maharramarsa bace, kamar yadda addinin Islama ya faci cewa haramun ne Namiji balagagge da Mace balagaggiya suna gogar junan su idan ba sun kasance ma’aurata ba, kamar yadda Tumba Bukar take shafar Adam a zango.
A yau ne mukaci karo da wata bidiyon jarumi Adam a zango da Tumba Bukar wanda ta kasance yarinyar sa tun asali, inda a cikin bidiyon zakuga yadda Tumba Bukar take taba jarumi Adam a zango.
Irin wadannan halayyar da jaruman kannywood suke bayyanawa yasa masana’antar kannywood kullum tana kan idon jama’a, domin wasu abubuwan da suke aikatawa haramun ne musulinci bai yarda da hakan ba amma suke yin abubuwan su gaba gadi.
Sannan kuma ba kowane jarumi ko jaruma ce a masana’antar kannywood suke jin kunyar wasu abubuwan da suke aikatawa ba, domin suna ganin wani abin da suke ai wayewace wanda hakan kuma kan janyo musu zagi da wulakanta ga jama’a.
Ga bidiyon nan domin ku kalla.