Labaran Kannywood

Ya Allah koda nayi aure na haihu kada ka nufi ‘yayana da shiga harkar fina-finan kannywood, cewar Ummi zezze

Tsohuwar jarumar fina-finan hausa wanda tayi sharafinta a shekarun baya da suka shude, Ummi Zeze, tayiwa ‘yayan ta wata addu’a wanda hakan ya zanto abin cece-kuce a gareta.

Kamar yadda kuka sani a yanzu ana yiwa masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood wani kallo wanda duk wani dan cikin ta ana yimasa wata fassara ta daban, walau na kirki ko kuma mutumin banza duba da yadda ake abubuwan badakala wasu lokutan a masana’antar.

Sai dai hausawa na cewa kyawun dan kwarai ya gaji uban sa duba da yadda zakuga mafiya wayan mutane suna daukar ‘yayan su su dorasu akan harkokin su na kasuwanci ko kuma wani waje da suke sana’a domin rufawa kai asiri.

Iyayen suna haka ne domin ganin yadda suna harkokin sana’ar da suke ya rufa msus asiri, shine suke zaton idan suka dora ‘yayan nasu suma hakan zata iya kasancewa a kan su.

Kamar yadda wasun ku suka sani Ummi Zeze tsohuwar jaruma ce a masana’antar kannyood wanda a yanzu haka ta daina harkar fina-finai ta barwa sabbin jarumai na yanzu, sai dai Ummi Zeze tayi wata wallafa a shafin ta na sada zumunta wanda hakan ya kusa janyo cece-kuce a kafafan sada zumuntar.

Inda take fadin cewa, kada Allah yasa ‘yayan ta su zamo jaruman fim, idan bazaku manta ba Ummi Zeze a kwanakin baya ta taba janyowa cec-kuce da tada kura a kafafan sada zumunta har ma ‘yan jarida sukayi shira da ita domin su tabbatar da abin data fada.

Ga wadanda suka labarin nata a kwanakin baya, Ummi Zeze tayiwa kanta barazanar kusa dalilin asarar wasu makudan kudade da tayi sanadiyqr wani mutumi ya damfare ta.

Bayan wannan labarin nata ya lafa, sai kuma a yau muka sami wannan labarin nata a shafin ta na sada zumunta, inda Ummi Zeze ta wallafa hoton ta tare da wani rubutu a kasa inda tayi shi cikin harshen turamci kamar haka.

Ya Allah here is my prayer, when ever get you me, MARRIED, And blessed me children, do not make them, FILM ACTORS.

Abin da jarumar take nufi shine, Ya Allah wannan ita ce addu’a ta duk lokacin da nayi aure kuma na haihu kada Allah yasa ‘yayan dana haifa su zama jaruman kannywood.

Jama’a da dama sun tambayi ba’asi akan wannan magana da Ummi Zeze tayi duba da kowa yasan da sana’ar fim Ummi zeze ta sami daukaka asirin ta ya ruhu amma a yanzu take fadin haka.

https://www.instagram.com/p/CVattkIMS45/?utm_medium=copy_link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button