Ashe wannan dalilin ne yasa jaruma Nafisa Abdullahi ta daina soyayya da jarumi Adam a zango
Kamar yadda kuka sani jaruma Nafisa Abdullahi shahararriyar jaruma ce a masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood wacce ta dauki lambobin yabo da dama, jaruma Nafisa Abdullahi ta amsa wasu tambayoyi da ‘yan jarida suka mata a yayin hira da sukayi da ita a kwanakin baya akan alakar dake tsakaninta da jarumi Adam a zango.
Jarumi Nafisa wanda a yanzu haka tana taka mushimmiyar rawa a cikin shirin nan mai godon zango wanda Tashar Saira Movies dake kan manhajar Youtube take harkawa a duk sati, LABARINA, jarumar ta bayyanawa ‘yan jaridar wata alaka dake tsakanunta da jarumi Adam a zango.
Da farko ‘yan jaridar sunji ta bakin jaruma Nafisa Abdullahi akan yadda take gudanar da rayuwarta da kuma kalubalen da take fuskanta a rayuwarta tun kafin ta fara harkar fim har kawo yanzu data shahara a cikin harkar fim, inda jarumar ta bayyanawa ‘yan jaridar cewa tafi kulla abota da Maza ba Mata ba.
A cikin jerin tambayoyin da ‘yan jarida suka yiwa jaruma Nafisa Abdullahi har da jita-jitar da take yawo a kafafan sada zumunta akan soyayyarta da jarumi Adam a zango,
Inda suke mata tambayar kamar haka.
Shin wai da gaske ne kan cewa akwai soyayya tsakaninki da bokin sana’arki jarumi Adam a zango, sai jaruma Nafisa Abdullahi ta kada baki tace eh akwai amma a lokutan baya amma yanzu babu wata alakar soyayya a tsakaninmu sai dai muna gudanar harkokinmu sabida abokin aiki na ne kuma muna aiki a masana’anta daya.
Sannan jarumar ta kara da cewa: Ko kun gammu a tare ba wai yana nufin soyayya ce a tsakaninmu ba kawai dai aiki ne ya hada mu, a shekarun baya dai munyi soyayya da shi amma ba yanzu ba.
Wanna itace amsar da jaruma Nafisa Abdullahi ta bawa ‘yan jarida a yayin da suka tattauna da ita kan yadda ta gudanar da rayuwarta da kuma kalubalen data fuskanta har ma da batun soyayyar su da jarumi Adam a zango.
Domin kuji cikekken bayani daga bakin jarumar sai ku kalli bidiyon dake kasa.