Daga yanzu na daina rungumar mata da sumbatar su a cikin fim da kuma rawa da waka, cewar jarumi Ali nuhu
Jarumi Ali nuhu ficaccan jarumi ne a masana’antar kannywood wanda wasu suke masa lakabi da sarkin kannywood, sannan kuma ya kasance Darakta mai shirya fina-finai masu dogon zango.
Sai dai duk wanda yasan harkar fina-finan wasan kwaikwayo to tana dauke da wasu abubuwa wanda mutum zai iya sa kan sa a cikin kunya da bakin jini wajan aikata abubuwan da basu dace ba, duba da yadda harkar fim ta gaji domin a yanzu sun dauki harkar fim a matsyin wayewa wanda idan baka nuna wasu halaye a cikin harkar ba to baka waye ba.
A cikin abubuwan da ‘yan wasan kwaikwayon suke aikatawa wanda duk yawan shekarun ka kama daga Namiji ko Mace to tabbas girman ka na iya faduwa wanda kowa zai ga kamar baka rike mutuncinka ba.
Cikin wadannan abubuwan suke kamar haka, Rawa a bainar jama’a a gidan gala, yawan hulta da ‘yan matan kowa yasan bana gari bane, wannan kadan daga ciki kenan.
Jarumi Ali nuhu wanda yake taka rawar gani a fina-finan masana’antar kannywood sannan kuma ya zamto babba a ciki wanda a yanzu haka ba’a kowane fim yake fitowa ba duba da yadda ya fara manyanta, inda jarumi Ali nuhu ya bayyana cewa daga yanzu ya dai na rawa da rungumar mata a cikin fim.
kamar yadda kuka sani a kwanakin baya wata bidiyon jarumi Ali nuhu ta bayyana inda a cikin bidiyon akaga yana sunbatar wata mata tare da rungumar ta al’amarin daya janyo cece-kuce a masana’antar kannywood, inda wasu daga cikin mabiyan sa a shafin sa na sada zumunta sukayi bakin ciki da wannan bullar bidiyon nasa.
Domin kuji cikekken labari kan wannan al’amarin sai ku kalli bidiyon dake kasa.
Allah kyauta
Allah yasa haka shine mafi alkhairi
Lallaikam kayi tinani Mai zurfi a nan Allah ya taimaka.
Allah shi kyauta
Alla yabaka Iko
Dahaka Haka
Allah yashirye shi, yasa yayi tuban gaskiy
Ameen summa ameen
Allah yasa hakan
Allah yasa haka ameen
Allah yaqara shiryardamu.