Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Jin dadin duniya yasa jaruma Hannatu S Usman tana dambe da karamin yaro

A wani faifai bidiyo da muka samo daga shafin instagram na jarumar kannywood Hanntu S Usman wanda a cikin bidiyon zaku ganta tare da wani yaro suna wasa, wanda har dambe suke gwadawa.

Advertising

Jaruna Hannatu Usman wanda tayi sharafinta a kwanakin baya a cikin shirin nan mai dogon zango wato Bugun Zuciya, wanda a yanzu haka ba’a shirin da ita ko mainene ya faru muma bamu sani ba.

Idan bazaku manta ba a kwanakin baya labarin jarumar ya bayyana kan cewa an koreta daga cikin shirin na Bugun Zuniya mai dogon zango, sai daga baya jarumar ta bayyana inda take bayani akan wannan labarin da ake yadawa na cewa na koreta daga cikin shirin, inda take bayyana gaskiyar al’amari akan abin da yake faruwa na daina ganinta da akayi a cikin shirin na Bugun Zuciya wanda wasu suke zaton ko an cireta daga cikin shirin.

Jarumar Hannuatu Usman ta bayyana cewa: Ba korarta akayi ba kawai dai ta fice daga cikin shirin ne da kanta duba da yadda tsarin shirin ya sabawa ra’ayinta kan abin data zaba a game da shirin, wannan shine dalilin da yasa jarumar ta cire kanta daga cikin shirin na Bugun Zuciya ba wai korarta akayi ba.

Advertising

Ga bidiyon jarumar nan tare da yaron domin ku kalla kuga yadda suke gudanar da wasa wanda hakan yana nuna cewa suna cikin farin ciki da kuma jin dadi, wanda dama haka ake so a kullum dan adam ya kasance cikin farin ciki da jin dadi ba wai kullum kana cikin bakin ciki ba.

Ga bidiyon nan sai ku kalla kai tsaye.

https://www.instagram.com/tv/CVfJgMMo1E8/?utm_source=ig_web_copy_link

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button