Advertising
Advertising
Labarai

Malamai sun sake kirkiro da wani al’amari akan maulidin da ake na nuna murna ga zagayowar ranar haihuwar Fiyayyan halitta S.A.W

A wannan lokaci da muke ciki maulidi ya zamo wani abu wanda baza’a daina cece-kuce a kansa ba haka kuma baza’a daina yin sa ba, kamar yadda kowa ya sani anayin maulidi ne domin nuna murna ga zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah .S.A.W.

Advertising

Kamar yadda malamai suka fadi cewa, an haifi Manzon Allah S.A.W ne a ranar sha biyu 12 ga watan Rabiul Auwal wato wannan watan da muke ciki, wanda bayn kwana bakwai 7 da haihuwar itace ranar suna kamar yadda malam Bahaushe ya tsara a al’adar sa.

Sai dai kuma malam Bahaushe yana da wata al’ada ta daban bayan wanda ake yanka dabbab sannan a dafa namanta ayi romo domin mai jego ta sha rashana, duk wani Bahaushe yana wannan al’adar ne bayan kwana biyar 5 da haihuwa inda ake kiran wannan al’ada da ” Kauri”.

Haka kuma bayan anyi kwana bakwai 7 da haihuwa akan sake yanka wata dabbar sannan a soya namanta, shi kuma wannan naman da ake soyawa na bayan kwana bakwai 7 da haihuwa shi ake kira da “Naman suna”.

Advertising

Tun lokacin da aka fara maulidi ake yanka dabbobi da yawa a ranar sha biyu 12 ga watan haihuwar Manzon Allah S.A.W, haka kuma bayan kwana bakwai 7 akan sake aiwatar da wannan shidimar wato ranar suna wanda malam Bahaushe yake kiranta da “Takutaha”.

Domin kuji cikekken labari akan yadda malamai suka kara kirkiro da wani al’amari akan da akeyi na nuna murna ga zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah S.A.W.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button