Advertising
Advertising
Labarai

Mawakin shugaban kasa Buhari Rarara ya bayyana cewa zai tsaya takarar dan majalistar tarayya a na Bakori da Danja

Shahararran mawakin siyasa wanda yayi fice wajan rerawa shugaban kasa Muhammad Buhari wakar dake sa al’umma ke kara sansa, Dauda Kahutu Rarara, ya bayyana cewa maganar da ake yayatawa kan tsayawar sa takarar dan majalista wanda zai wakilci kananan hukumomin Bakori da Danja gadkiya ne ba karya ake ba.

Advertising

A wata zantawa da mawaki Rarara sukayi da shafin Leadership Hausa a Katsina kan wasu batutuwa da suka shafi wakokin sa musamman akan wakar da yace talakawa ne suka biya kudin wakar da kuma batun tsayawar sa takara.

Mawaki Rarara ya kara da cewa: A yanzu haka akwai batun sabuwar wakar da yayi wanda talakawa suka biya kudi domin bayyana aiyukan shugaban kasa Muhammad Buhari, sannan yace a kwanan nan zai fara bin jahohin Nageriya domin nuna irin aiyukan da shugaba Buhari yahi.

Rarara ya kara da cewa: Idan Allah yasa na kammala aiyukan dake gabana to zan tsaya takarar dan majalistar tarayya na kananun hukumonin Bakori da Danja, idan kuma wadannan aiyukan suka sha gabana sai kuma a duba batun zuwa nan gaba.

Advertising

Sannan ya bayyana cewa: ya bukaci ya gano aiyukan shugaban kasa Muhammad Buhari guda 90 amma sai ya gano guda 900 wanda yake ganin aikin yana da yawa, amma idan ya sami damar kammala wadannan aiyukan zai dawo kan maganar tsayawa takarar sa wanda tuni ya fara yawo a gidajen siyasa.

Ya sake bayyana cewa: Zaben shugabannin da aka gudanar a satin daya gabata a Katsina abin ya masa kyau sosai, sabida haka yana fatan wannan zaben zai taimaka wajan kara samin nasarar jam’iyyar su ta APC a zabe mai zuwa.

Haka kuma Rarara ya yaba da tsarin da aka bi wajan samar da shuwagabannin wanda ya fadi cewa abin yayi matukar burgeshi, kuma a kasar Nageriya babu inda aka yi abin daya dace kamar na jihar Katsina inda ya kara da cewa ko shugaban kasa Buhari ya yaba da kokarin Gwamna Masari akan hakan.

Dauda Kahutu Rarara ya kara da cewa: Idan ka duba da kyau tun a zaben shuwagabannin ta matakin runfuwa da kananun hukumoni dana jihar babu wanda ya furta cewa bai yarda da tsarin da aka yi ba, sabida haka wannan shine ake kira da shugabanci sannan kuma Gwamba Masari yayi kokarin wajan hada kan ‘yan jam’iyyar APC a jihar Katsina.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button