Advertising
Advertising
Labarai

Mun rasa Namijin da zai aure mu shiyasa muka auri junanmu domin mu biyawa kammu bukata, Labarin wasu ‘yan mata 2

kamar yadda shafin Apahausa ya wallafa labarin wasu ‘yan maya guda biyu 2 ‘yan asalin kasar Kamaru wanda suka auri junansu bayan da suka rasa Namijin da zai aure su.

Advertising

A cikin wani bidiyon ‘yan matan da tayi ta yaduwa a shafin Telegram ‘yan matan sun bayyana yadda suke aiwatar da mu’a malarsu irin ta Miji da Mata, duk da sun kasance jinsi daya amma duk da haka suke aikata irin abin da ma’aurata Namiji da Mace suke aikatawa.

Dalilin bayyanar wannnan bidiyon nasu jama’a sukayi ta musu cece-kuce tare da tambayoyi akan dalilin da yasa suka auri junan nasu, alhali kuma ga maza nan wanda suke neman matan da zasu aura.

A cikin ‘yan matan kowacce sunanta ya bayyana daya sunanta Laraba daya kuma sunanta Hadiza, sun bayyaan dalilin da yasa suka auri junan nasu sabida sun rasa mijin aure, wanda kuma suna cikin matsananciyar sha’awa ta dalilin haka zasu iya shiga wani halin.

Advertising

Sabida haka ne yasa suka yanke shawarar su auri junan su amma babban dalilin da yasa suka fara harkar Madigo har takai ga sun auri junan su shine, sun nemi Namijin da zai aure su amma basu masu ba.

Daga karshe da suka rasa yadda zasuyi shine suka fara neman junan su wanda har takai ga sunyi nisan da basajin sha’awar Namiji kwata-kwata sai ‘yan uwansu mata kawai.

Wannan al’amarin ba karamin al’amari bane domin ‘yan mata da yawa wanda basa tsoron Allah zasu iya amfani da wannan damar domin ganin sun shiga irin wannan harkar ta madigo, Allah ya kawo mana karshen wannan musifar.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button