Bayan Rahama Sadau ta dawo daga kasar India ta wallafa hotunan da suka janyo mata cece-kuce
Shahararriyar fina-finan Arewacin Nageriya da kuma Kudanci wanda a yanzu tana gudanar da wani shiri a sakar India wato, Rahama Sadau, ta wallafa wasu sabbin hotunanta a shafinta na sada zumunta instagram wanda jama’a suka tofa albarkacin bakinsu kan wadannan hotuna nata.
Idan baku manta jaruma Rahama Sadau ta fita kasar India domin shirya wani fim mai suna Khuda Hafeez, inda jarumar ta wallafa wasu hotunanta tare da ‘yan kasar India wanda zasuyi shirin tare har ta saje da su domin irin yadda suke shigar su itama haka tayi.
Bayan ta dawo gida Nageriya sai kuma ta sake wallafa wasu sabbin hotuna wanda take sanye da bakaken kaya wanda dama kana ganin ta kasan ta saba amfani da irin wadannan kayan data sanya a jikinta.
Ga hotunan a kasa domin ku kalla.
Allah ya shiryi rahama sadau ta game gaskiya akan irin wadannan kaya da take sakawa da duk Mai irin Hali Nata yasa suna gane gaskiya tun kafin lokaci kure musu ameen ya Allah