Labarai

Hukumar Hisbah dake jihar Kano ta kama matashin da yayi yunkurin sayar da kansa Naira Miliyan 20M sabida talauci

Hukumar hisbah dake jihar Kano ta kama wannan matashin mai shekaru 26 wanda yayi yunkurin sayar da kansa sabida yaje jihar Kano bai sami damar ganin Naziru Sarkin Waka ba.

Idan bazaku manta ba a makon daya gabata ne labarin wani matashi mai suna Aliyu Idris ya karade kafafan sada zumunta, inda matashin yake kokarin sayar da kansa har ma yake yowa da kwali a hannunsa yana neman wanda zai saye shi Naira Miliyan 20.

Kwamandan ‘yan Hisbah Haruna Ibn sina ya tabbatarwa da BBC kama matashin inda yake bayyana cewa abin da matashin ya aikata haramun ne.

Yaci gaba da cewa: Mun kama shi tun ranar Talata sannan kuma ya kwana a hannun mu sabida abin da Aliyu ya aikata haramun ne a addinin musulinci, domin baka da damar sayar da kanta ako wani irin hali kake.

Aliyu Idris wanda ya kasance Tela ne mai dinki ya bayyana cewa, yana cikin rashin kudi ne shi yasa ya yanke wannan shawarar domin ya sayar da kansa Naira Miliyan 20, sannan kuma yayiwa duk mutumin da zai saye shi shidima da zuciya daya.

Kafin a kama matashin sai da ta bayyanawa ‘yan jaridar Kano cewa, ya yanke shawarar sayar da kai na ne sabida talauci idan na sami wanda zai saye ni to zan bawa iyayena Naira Miliyan 10 sannan kuma na biya Naira Miliyan 5 ga Gwamnati a matsayin kudin haraji, Naira Miliyan 2 kuma ga duk wanda ya taimakamin wajan neman wanda zai saye ni sauran kuma sai na ajiye su domin yin amfanin yau da kullum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button