Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Kalli yadda shahararrun mawakan kannywood Ado gwanaj, Ali jita, Naziru sarki waka suke cashewa a wajan bikin abokin su

Kamar yadda kuka sani masana’antar kannywood masana’anta ce da take da tarun shahararrun jaruman wasan kwaikwaiyo da kuma mawaka, inda suke hada kansu a duk lonacin da shagalin bikin wani ya taso daga cikin su suna haduwa waje guda domin taya shi murnar bikin nasa.

Advertising

Sai a yau kuma muka sami wata bidiyo wanda tashar Tsakar gida ta wallafa inda a cikin bidiyon zakuga jaruman masana’antar kannywood mawaka suna cashewa a bikin wani abokin mawaki Naziru M Ahmad wanda kuka fi sani da Naziru Sarkin waka.

A cikin mawakan da suka halarci wannan wajan shagalin bikin na abokin Naziru Sarkin waka sun hada da, Ali jita, Ado gwanja, Nazifi asnanic tare da shi kansa Naziru Sarkin waka, inda a wajan bikin suke rera waka tare da cashewa kamar yadda zakugani a cikin bidiyon dake kasa.

mawakan sun halarci wajan bikin ne domin taya murna ga abokin abokin sana’arta su wanda dama sun saba irin haka a duk lokacin da daya daga cikin su yake yake gudanar da wani biki sukan hada kai domin tayashi murna, wanda hakan yana kara musu zaman lafiya tare da hadin kai wanda ta dalilin haka kowa yake sabawa da kowa a cikin su shi yasa wani lokacin zakuga kamar ma ‘yan uwan juna ne.

Advertising

Domin kuga yadda shahararrun mawakan kannywood suke cashewa a wajan shagalin bikin sai ku kalli bidiyon da muka ajiye muku a kasa.

Ga bidiyon nan domin ku kalla kai tsaye.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button