Tirkashi: An bankado wani boyayyan sirri akan jarumi Adam a zango kan abin da yayiwa marayu
Kamar yadda wani mutumi yayi tsokaci a shafin sada zumunta na Facebook akan jarumi Adam a zango inda ya wallafa wani dogon bayani kamar haka.
Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan kana lafiya, Allah sanya haka Ameen, Wai ina aka kwana game da maganar marayun da Adam a zango ya dauki nauyin karatun su a garin zariya.
Bayan haka ba tare da bata lokaci ba ba rubuta maka wannan da nufin jin inda aka kwana game da babban alkairin da kayi da kayi ikirarin ka aikata a bara a wanan, Oktoba 2020, inda ka sanar da al’umma cewa ka fitar da zunzurutun kudade kimanin Naira Miliyan 47 domin daukar nauyin karatun yara marayu sama da guda dari 100, a wata makaranta mai zaman kanta mai suna, Professor Ango Abdullahi College.
Babban dalilin da yasa na tado maka da wannan batun shine, sabida a bara dai-dai wannan lokacin al’amarin naka ya tada kura a kafafan sada zumunta na soshiyal midiya da kuma jaridu har ma da mujallu.
Akwai kokwanto kan al’amarin inda har wasu ma suke karyata ka wasu kuma suka nemi taba mutuncinka, idan baka mance ba ni kai na daga jaridar Aminiya na kiraka a waya sau uku 3 baka daga ba kuma na turo maka tes amma kaki amsa tambayar mu, haka muka gaji muka buga al’amarin ta hanyar abin da muka samu daga hukumar makarantar da kuma wani bangare na fadar mai martaba Sarkin Zazzau.
Wannan kadan daga cikin abin da mutumin ya wallafa domin kuji cikekken labari sai ku kalli bidiyon dake kasa, ta haka ne zakuji dukkan abin da mutumin ya wallafa akan jarumi Adam a zango.
Ga bidiyon nan domin ku kalla.
Allah yabamu saa
Bashirumusa@email
Abdul bashir