Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Yanzu-Yanzu: Rahama Sadau ta saki sabuwar bidiyo tana motsa jikinta dalilin kiba ta mata yawa

Kamar yadda kuka sani Rahama Sadau ficacciyar jarumace a masana’antar kannywood wanda ta dauki lambobin yabo, wanda a yanzu kuma ta daina fitowa a fina-finan na kannywood inda ta koma kasar waje da yin fim din ta wato India.

Advertising

Rahama Sadau ta wallafa wata bidiyo a shafunta na instagram inda muka ganta tana motsa jiki wanda hakan yana da kyau koda da yaushe ka zamto cikin motsa jiki yin hakan hana karawa mutum lafiya matuka.

Idan kuka dubi jaruma Rahama Sadau a yanzu tayi girman da yakamata tana motsa jikinta domin ta zama katuwa har ma wasu suke mamakin griman nata duba da yadda take a shekarun baya wanda ba kowane yake tunanin zatayi wannan girman ba, amma a yanzu abin ya bawa mutane mamaki inda girman nata ma kamar karuwa yake sabida haka take motsa jikinta domin ta sami sassauci.

Wannan motsa jiki da Rahama Sadau take masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa yana da matukar amfani ga lafiyar jikin dan adam, domin kuwa idan mutum tumbi ya masa yawa ko kiba tana damunsa to idan kana wannan tirainin na motsa jiki zaka iya dawowa dai-dai.

Advertising

Shi yasa zakuga turawa da larabawa suna sanya irin wadannan abubuwan na motsa jiki a gidajansu wanda hakan ba karamin taimaka musu yake ba, domin yana kara musu lafiya da kuma karfafa musu garkuwar jiki dannan yana kashe musu kananan cututtuka.

Ga bidiyon nan domin ku kalla kuga yadda jaruma Rahama Sadau take motsa jikinta.

Advertising

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button