Ficacciyar mawakiya a kannywood Aisha Isah Usman wacce aka fi sani da Ummi Kano mai daraja ta bayyana dalilin da yasa suka rabu da mijinta
Ficacciyar mawakiya a masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood wanda take rera wakokin siyasa kala-kala, Aisha Isah Usman wacce aka fi saninta da Ummi Kano mai daraja, ta bayyana dalilin rabuwar su da mijinta bayan sun sami arziki na haihuwar ‘yaya guda biyu 2 wanda har yanzu tana kewar mijin nata domin rabuwar da sukayi ba asan ransu ba.
Aisha Isah Usman wato Ummi Kano ta bayyana kahan ne a lokacin da suke tattaunawa da wakilin jaridar Damukaradiyya dangane da yadda ta gudanar ta raywarta ta baya kafin ta shiga harkar waka.
Sai Ummi Kano take bayyana musu cewa: Duk da cewa na fara waka kafin nayi aure tun ina makaramtar Islamiyya, bayan kuma nayi aure sai na daina harjar wakar amma bayan mun rabu da mijina aure na ya mutu sai na dawo harkar wakar.
Dangane da abin daya shafi mutuwar auren ta kuwa ta bayyana cewa: Allah ne ya kawo rabuwar mu da mijina ba wai don bana sansa ba, muna matukar son junan mu ni da mijina sai dai sabida wani sabani na akida tsakanin gidan mu da mijina yasa aka raba auren mu, kuma lokacin da aka raba auren namu yana kuka nima ina kuka haka muka rabu da juna sai dai har yanzu muna yiwa juna fatan alheri.
Daga karshe Ummi Kano ta bayyana cewa: A yanzu babban burina dana mahaifiyata shi ne na sami miji nayi aure, kuma ina fatan Allah ya cika mini burina dana mahaifiyata.