Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Jaruma Fatima Hamza ta cikin shirin Izzar so ta tona asirin wasu mutane yanzu-yanzu

Shahararriyar jaruma a cikin shirin fim din nan mai dogon zango wanto, IZZAR SO, wanda ake harkashi a tashar Youtube sai suna, BAKORI TV, Fatima Hamza ta karyata wasu mutane wanda suke amfani da sunanta wajan damfarar mutane.

Advertising

Irin wannan al’amarin ba yanzu aka fara shi ba domin anjima ana amfani da sunan wasu jarumai na masana’antar kannywood wajan damfarar mutane ana karban kudade a hannun su domin a sanya su a harkar fim ko kuma wani abu makamancin haka.

Hakan ta faru akan Darakta abubakar bashir mai shadda inda wani mutumi ya fake da sunan sa ashafin Facebook yana damfarar mutane yana karbar kudaden su da sunan zai sanya su a cikin harkar fim, saj daga baya Darakta Abubakar Bashir ma shadda ya bayyana a cikin wata bidiyo inda yake bayani akan cewa bashi bane kawai dai wani ne yake damfarar su tana karbar kudin su, wanda akan zai iya bata masa suna a idon duniya.

Sannan akwai jaruma da hakan ta taba faruwa a kansu kamar su, jaruma Hadiza gabon, jaruma Aisha Aliyu Tsamiya, Teema makamashi da dai sauran su.

Advertising

Wadannan jaruma sun kasance ‘yan kasuwa ne wanda hakan ya zame musu dole sai sunyi hulda da jama’a ta kudi, sannan sukan hadu da wasu mutanen ta online domin yin kasuwancin ta dalilin hakan sai kaga wani ya bude shafi da sunan su yana damfarar mutane.

Domin kuji cikekken bayani sai ku kalli bidiyon da muka ajiye musu a kasa.

https://youtu.be/_IFjqomhq10

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button