Labaran Kannywood

Jarumin wasan kwaikwayo Baba Ari ya bayyana halin daya shiga wanda ya kusa mutuwa a lokacin da yaje Saudiyya Dawafi

Shahararran dan wasan kwaikwayon nan wanda ya jima yana sharafin sa wato Baba Ari ya bayyana cewa, akwai lokacin da yaje saudiyya dawafi sai da yakusan mutuwa sabida cunkoson al’umma.

Ficaccan jarumin wasan kwaikwayon wanda kowa yasan shi da wannan sunan da ake kisan sa da shi, Baba Ari, ya bayyana tarishin rayuwar sa a shirar da sukayi da jidan jaridar BBC Hausa wanda dama jidan jaridar na BBC Hausa sun saba tattaunawa da manyan mutane ko ‘yan siyasar kasar nan ta Nageriya ko kuma shahararrun jaruman kannywood.

A cikin shirar da sukayi da BBC Hausa ya bayyana wani alabri wanda bazai taba mantawa da shi ba a rayuwar sa, wanda lokacin da yake kasar saudiyya domin yayi dawafi ya tarar da cunkoson al’umma inda a wajan aka matse shi taji numfashin sa yana yin sama-sama kamar zai mutu.

Sannan kuma Baba Ari ya bayyana irin kalubalan daya fuskanta a rayuwar sa kafin ya shiga harkar wasan kwaikwayo, haka kuma ya bayyana kalubalan daya fuskanta bayan ya shiga harkar ta wasan kwaikwayo.

Baya ga wannan kalubalen daya fuskanta ya sake bayyana irin nasarorin daya samu a harkar ta fim, inda yake bada shawara ga matasa da kuma masoyansa wanda suke kallon shirin fina-finan sa.

Domin kuji cikekken bayani sai ku kalli bidiyon da muka ajiye muku a kasa.

https://youtu.be/hOcaZsPZfSI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button