Advertising
Advertising
Labarai

Matashin da yayi yunkurin sayar da kansa dalilin baiga Naziru Sarkin waka ba daga karshe sun hadu

Kamar yadda kuka sani a kwanakin baya labarin wani matashi dan jihar Kaduna ya tulla inda yake yunkurin sayar da kansa akan farashin Naira Miliyan 20M, sabida yayi tattaki har zuwa jihar Kano domin yaga masoyinsa Naziru M Ahmad wanda kuka fi sani da Sarkin waka amma hakan yaci tura.

Advertising

Bayan matashin mai suna Aliyu Idris ya yankewa kansa wannan mummunan shawarar ta sayar da kanta domin ya huce haushin rashin nasarar da yayi ta ganin Naziru Sarkin waka, sai Allah ya taimake shi inda zuwa wasu kwanaki Allah ya nufeshi da ganin wanda yake burin su hadu wato Naziru M Ahmad Saekin waka.

Bayan haduwar tasu da shahararran mawaki Naziru M Ahmad Sarkin waka har hotuna suka dauka wanda hakan yana nuna cewa, shima Naziru Sarkin waka yaji dadin haduwa da wannan matashin domin da basu hadu ba matashin zai iya saka kansa cikin wani hali wanda rayuwar zata lalace.

A cikin hotunan da zaku kalla zakuga yadda matashin tare da Naziru Sarkin waka suka rungumi juna da kuma bayyana farin ciki sabida sun hadu da juna, haka kuma shima matashin idan kuka dubi fuskar sa zakuga a cike take da farin ciki domin kuwa burin sa ya ciki na samin damar ganin shahararran mawakin Naziru M Ahmad Sarkin waka.

Advertising

Ga hotunan nasu nana a kasa domin ku kalla.

Advertising

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button