Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Mawaki Nazifi Asnanic ya karyata abin da jaruma Hadiza gabon ta fada a kansa sannan kuma yace sai ya rama

Ga wadanda suke yawan bibiyar shafukan sada zumunta na jaruman kannywood musamman ma shafin Istagram zasuga jaruman sun maida hankali wajan wallafa zafafan hotunan su musamman jarumai Mata, domin wasu daga cikin su zakuga suna bikin murnar zagayowar ranar haihuwa wato “Happy Birthday”.

Advertising

Sai a yau kuma muka bibiyi shafin shahararran mawakin kannywood Nazifi asnanic inda ya wallafa hoton sa tare da yana mai murnar zagayowar ranar haihuwar sa, inda wasu daga cikin jaruman kannywood suka wallafa hoton nasa a shafukansu na sada zumunta Istagram kamar yadda shima ya wallafa.

Da farko jaruma Hadiza gabon ita ta fara wallafa hoton mawakin inda take cewa Happy Birthday Nazifi Asnanic.

https://www.instagram.com/p/CViAAynLa9d/?utm_medium=copy_link

Bayan da jaruma Hadiza gabon ta wallafa wannan hoton na mawaki Nazifi Asnanic sai abin ya bawa jama’a mamaki ganin yadda duk lokacin da wani jarumi ko jaruma zasuyi “Happy Birthday” na murnar zagayowar ranar haihuwar su sune kan gaba wajan fara wallafa hotunan nasu, sannan sai ‘yan uwa da kuma abokan arziki su fara wallafa fotunan.

Advertising

A lokacin da jaruma Hadiza gabon ta wallafa wannan hoton sai jarumi Hassan Giggs yace shima zai wallafa hoton wata kila mawaki Nazifi Asnanic din ne bai sani ba, amma bayan haka munga wata bidiyo a shafin mawaki Nazifi Asnanic din inda yake karyata wannan batun na cewa yau ba ranar murnar zagayowar ranar haihuwar sa bace wato “Happy Birthday “, Kamar yadda zakuji daga bakin sa a cikin bidiyon, ga bidiyon nan domin ku kalla.

Sannan kuma mawaki Nazifi Asnanic ya bayyana cewa tunda jaruma Hadiza gabon tayi masa haka shima sai ya rama.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button