Labaran Kannywood

Rikici ya barke a tsakanin jaruman shirin Izzar so Aisha Najamu, Fatima Hamza P.A da Nana

Kannywood masana’anta ce wanda ta tara jarumai da yawa mata da maza wanda ake shirya fina-finai da su, kamar yadda kuka sani ba sabon abu bane yawan yin rikici da janyo cece-kuce a tsakanin jaruman na jannywood musamman ma jarumai mata, inda zakuga sun bayyana kansu a soshiyal midiya suna fadin maganganu kala-kala daga bisani kuma sai kaga sun shirya tsakanin su da kan su.

Wannan labarin ya rankaya ne akan wasu jarumai na kannywood inda ake haska wasu daga cikin a shirin nan mai dogon zangi na Izzar so, a cikin su akwai Aisha Najamu da kuma Fatima Hamza wacce aka fi sani da P.A sai dayar wacce aka fi sanin ta da Nana.

A labarin da muka samu wanda yake yawo a kafar sada zumunta na Insragram wanda jarumar shirin Izzar so Fatima Hamza wacce ake kura da P.A, ta wallafa wata bidiyo inda take bayyana tarihin rayuwar ta sannan kuma take bayyana wasu abubuwa da suka shafeta wanda ya kamata mutane su sani a kanta.

A bayan da jarumar rayi a cikin bidiyon da ta wallafa zakuji yadda take cewa, akwai wata a cikin shirin Izzar so wanda shirin na Izzar so yayi mata rana amma bayan haka sai take jamusu aji sabida yanzu ta zama wata, bayan kuma ta dalilin shirin na Izzar so ta sami wannan daukakar wanda har dumiya ta santa amma take nuna musu halin ko in kula tsakanunta da abokan aikin nata na shirin Izzar so da kuma wanda suke shirya shirin.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin wanda ake rikicin da ita da kuma yadda abin ya samo asali.

Fa bidiyon nan domin ku kalla.

https://youtu.be/XBV6QDKIPwU

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button