Wani barawo ya hallaka kansa yayin da yaje satar wayoyin wutar lantarki cikin transfoma
Wani barawon wayoyin lantarki ya gamu da ajalinsa a yayi da yashiga cikin Transfoma a jihqr Kano, al’amarin ya faru ne a ranar Laraba yayin da darawon da mutanen sa suka far ma harabar kamfanin wutar dake kan hanyar Dawanau-Dawakin Tofa.
Bayan abin ya faru sai sauran mutane barawon suka tsere inda sukabar gawar a wajan inda wutar ta rike ta, al’amarin ya faru ne safiyar ranar Laraba 27 ga watan Oktoba, a lokacin da barawon tare da mutanen sa suka kai mamaya harabar kamfanin wutar lantarkin dake hanyar Dawanau-Dawakin Tofa dake hanyar jihar Kano.
Shugaban sashin sadarwa na kamfanin mai suna, Ibrashim shawai ya tabbatar da faruwar al’amarin, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwauto.
Ibrashim shawai ya kara da cewa: Barawon ya taki rashin sa’a a lokacin da aka dawo da wutar lantarkin cikin Transfoma.
Kakakin kamfanin wutar lantarkin ya koka akan masu sace-sacen wayoyin wutar lantarkin wanda dama sun jima suna satar kayan ma’aikatar.
Ibrashim shawai ya kara da cewa: Ina addu’ar Allah yasa wannan ya zama izina ga sauran wadanda suke da niyyar sace-sacen kayammu dana ma’aikatar.
Da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Kiyawa ya tuntube shi ya bayyana cewa, suna kan binciken lamarin, kamar yadda Daily post tayi rohoton.
Wannan shine abin daya faru da barawon alokacin da yaje satar wayoyin wutar lantarki.