Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Tsofaffin Mawakan Kannywood (5) Mata Wanda ba kowa yasan Fuskokin su ba.

Maryam sale Muhammad da akafi sani da Maryam fantimoti Shahararriyar Mawakiya wace itama tana cikin jerin manyan mawaka a Masana’antar Kannywood.

Advertising

Mutane da dama basu san Fuskar maryam ba, illa kawai suna jin wakokinta da kuma lakabin fantimoti da ake kiranta dashi, kasancewar ba harkar film takeyi ba, illa wakoki kawai da takeyi acikin Finafinai.

A bincike da tashar Hausa Daily News ta gabatar, ta gano cewa Maryam ta kwashe akalla kimanin shekaru ashirin tana waka a Masana’antar Kannywood, hakan yasa ake mata lakabi da Maman mawaka.

Maryam tayi wakoki da suka shahara irin su Wakar Uwar gida shaba, Dijangala, jigida da dai sauran su.

Advertising

Bayan wakokin Finafinai da takeyi tana yin wasu wakokin na daban wanda suka hada da Wakokin sarakuna, Attajirai da kuma wakokin yabon manzon Allah SAW.

Maryam fantimoti

Maryam a baba wacce akafi sani da maryam sangandale daya daga cikin shahararrun mawaka wanda sun dade suna bada gudumuwa acikin finafinan hausa na tsawon lokaci.

Maryam ta rera wakoki da dama tare da manyan mawaka irin su misbahu m ahmad, mudassir kasim, sadi sidi sharifai, da kuma Aminu alan waka.

daga cikin wakokin data rera sun hada da wakar sangandale, sanafahna, jinsin mata da sauran su.

Bayan harkan waka da takeyi maryam babbar yar a kasuwa ce domin kuwa kasuwancin nata ya ketara har kasashen waje inda take siyo kaya daga kasashe irinsu dubai, india, cotonou da sauran su.

maryam sangandale

Idan masu bibiyar mu a wanan shafin zasu tuna mun kawo muku rubutu akan ta, sannan kuma wannan mawakiya ta rasu tin a shekara ta 2014 bayan da tasha fama da rashin lafiya.

Hausa Daily News ta gano cewa Tarihin Mawakan Kannywood mata bazai cika ba, ba tare da ambatar sunan wannan mawakiya ba, domin kusan itace mace ta farko data fara rera wakoki acikin finafina hausa.

Marigayiyar Ta bada gudumuwa ba kadan ba a Masana’antar Kannywood, bayan wakoki da takeyi takan fito a matsayin jaruma.

Acikin wakoki da marigayiyar ta rera sun hada da wakar film din badali, Mujadala, Ki yarda dani, da sauransu a karshe muna Mata Addu’a Allah yakai haske kabarinta ameen.

Sakna gadaz Itama fitacciyar mawakiya ce a Masana’antar Kannywood sannan kuma wannan mawakiya haifaffiyar garin kano ce.

Ta kwashe shekaru da dama tana rera wakokin acikin finafinan hausa, wannan mawakiya baga wakokin Finafinai kawai ta tsaya ba domin kuwa itama tana rera wakokin yabon manzon Allah SAW.

Mutane da dama a yanzu ba kowa yasan cewa tana rera wakoki acikin finafinai ba, sannan kuma a bangaren finafinai tayi fice ne acikin film din rabi’atul adawiyya.

Sakna gadaz

Binta labaran wadda akafi sani da fati niger, duk da kasancewar wannan mawakiya yar jamhoriyar niger ce, amma kusan dukkan al’amuran ta da harkokin ta sun dawo cikin Nigeria.

Faty niger tana cikin jerin Tsofaffin mawakan Kannywood wanda sun kwashe lokuta masu tsawo suna gabatar da wakoki acikin finafinan hausa.

Hakan yasa koda lissafi, ba za’a wuce sunan taba, cikin manyan Wakoki da faty niger tayi wanda suka samu karbuwa wajen jama’a sun hada da Wakar Girma Girma, Uwa, Zancen soyayya da sauran su.

Faty niger

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button