Advertising
Advertising
Labarai

Wata Dattijuwa ‘yar kasar Burtaniya mai shekaru 82 tayi wuff da matashin saurayi dan shakaru 36

Wata dattijuwa ‘yar kasar Burtaniya mai shekara 82 tayi wuff da wani matashin dan shekara 36 wanda bayan sunyi auren ta bukaci sai anba shi biza ya koma kasar Burtaniya da zama inda take.

Advertising

Kamar yadda shafin Daily Nigerian suka ruwaito cewa: Gyatumar mai shekaru 82 ta kafe dole sai an bawa Angon nata biza yakoma inda take da zama.

Baturiyar ‘yar kasar Ingila mai suna Irus Jones tace, idan ba’a bawa mijinta Mohamed Ibrashim biza to sai rijiya.

Baturiyar ta hadu da wannan santalelen saurayin data aura a shafin Facebook daga nan kuma tayi tattaki har zuwa kasar Masar inda matashin yake domin ta hadu da shi.

Advertising

Bayan haduwar su sai sukayi aure inda ya koma kasar Burtaniya da zama tun bayan wannan lokacin ake ta ga maciji akan angon nata bashi da biza domin tarewa da Amaryar tasa a kasar Burtaniya.

A watan gobe ne dai ake sa ran ofishin jakadancin kasar Burtaniya zai dauki mataki akan batun bizar Angon Baturiyar wato Mohamed.

Ga hotunan da suka dauka tare domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button