Advertising
Advertising
Labarai

‘yan sanda sun damke wani mutumi kan laifin turawa matar aure sakon da zai iya haddasa tashin hankali tsakanin ta da mijinta

Wani mutumi ya shag hannun ‘yan sanda bayan ya turawa matar aure wani sako wanda ta dalilin hakan zai iya sa auren matar ya mutu.

Advertising

‘Yan sanda sun damke mutumin da laifin mai shekaru 38 sannan kuma tuhumeshi da babban laifi na kokarin tada tarzoma tsakanin matar aure da mijinta.

Al’ummar kasar Nageriya da dama sun tofa al’barkacin bakin su kan wannan al’amarin dakr faruwa tsakanin mutumin da jami’an ‘yan sanda dalilin ya kusa saddasa tashin hankali a tsakanin ma’auratan.

Wani mutumi dan kasar Nageriya mai suna Siriku Oluwaseun Jamiu ya fada hannun jami’an ‘yan sanda akan aikata laifin turawa matar aure wani sako wanda kan iya haddasa rigima tsakanin matar da mjiinta, inda ya rubuta mata sakon kamar haka, Ina kwana Baby.

Advertising

Hukumar ta bayyana cewa ya turawa matar wannan sakon ne a ranar 19 ga watan Satumba 2021, a hoton da @Instablog9ja ta wallafa, Mutumin ya tura wannan sakon ta manhajar Whatapp ne wanda hakan ya sabawa sashe na 249 na dokokin jihar Ogun.

Acewar su abin da mutumin mai suna Siriku yayi kan iya zama matsala ga auren matar mai suna, Opeyemi da mijinta Akintunde.

Advertising

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button