Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Gaskiya ta bayyana akan zargin da akewa jaruma Rahama Sadau na komawa addinin kiristanci

Kamar yadda kuka sani Rahama Sadau ficacciyar jaruma ce a masana’antar kannywood da kuma Nollywood wanda ta kasance tana aikata abubuwan da take janyowa kanta maganganu marasa dadi.

Advertising

Musamman al’adar da jarumar ta dauka wanda ba irin al’adun ‘yayan musulmai bane tana koyi da wasu abokananta wanda sun kasance ba musulmai ba.

Jarumar takan yi shigar kayan da addinin musulinci bai yarda da shi ba sannan kuma ta wallafa su a shafin na sada zumunta Instagram, inda al’umma fadin abubuwa da dama wanda babu dadin ji ga jarumar.

Jaruma Rahama Sadau tayi wata wallafa a shafin ta na Tweeter kamar haka, a lokacin da wani mutumi ya mata tambaya sannan ta mai da masa da amsa cikin gaggawa.

Advertising

Bayan Rahama Sadau ta wallafa wannan bayanin sai wani matashi yayi mata tambaya da cewa, naji ance kin koma addinin kiristanci shin da gaske ne.

Wannan cece-kucen ya samo asali ne tun bayan bullar wannan labarin a kwanakin baya a lokacin da wani mawakin kasar waje mai suna, Akon, ya kirata domin ya taimaka mata dalilin korarta da akayi daga masana’antar kannywood.

Dalilin wannan korarta da akayi daga masana’antar kannywood shine wakar da sukayi tare da mawakin hausa Hiphop wato Classic, inda aka ga jarumar ta rungume shi ta baya.

To wannan al’amarin yasa akayi ta zargin jarumar da komawa addinin kiristanci duba da wadannan abubuwan da take aikatawa, sannan kuma jarumar ta dauki al’adun mutanen kudancin Nageriya abokadanta tana amfani dasu.

Har kawo yanzu jaruma Rahama Sadau bata daina sanya kayan da zasu janyo mata cece-kuce ba domin a yanzu haka ta sake wallafa wasu sabbin hotunan ta a shafin nata na instagram, kamar yadda zaku gani a kasa.

Advertising

52 Comments

 1. Gara ma ta fita daga musluncin ta daina jawa musulmai zagi tunda rayuwar data zaba kenan wawuye duk yadda akai ba’aje islamiya ba dama, da haihuwar irin wa’annan gara barinsu tunda bakidau darasiba kan batanci da akaiwa ma’aiki sakamako ballagazan cinki bazamu raga miki sakarya sauna kucaka

  1. I don’t know why some think that it’s religion will take you to heaven,the only way is to believe in Jesus Christ He is the only way and the truth no one go to the Father except through him,so let every body decide un what to do, but all what I know is went Jesus will come back for the second time, every body will give account of what he or she don here un earth remain blessed

   1. We Muslim we are more Christian then self bcos we respect Jesus we believed with him,but in thise varse=Jesus said i can of my self do nothing as i hear i judge,and my judgement is just bcos i seek not of my own will, but the will of father,who send me.

 2. Ni na kasa gane kan labarin ,abinda nakeso in fahinta ,shin ta fice ne ko tananan a addininta ?
  In har tananan ina bata shawara Duniya dai ba karya bace tunda gata a cikinta to inda ta tsinci kanta Duniya haka kwatsam zata ganta a Lahira inda lissafin alkhari ko sharri zai zabawa Mutun wajen zama
  Allah SWT ya cecemu.

  1. gaskiya.magana wanan mace tana jawo cece kuce gaskiya shawarar da na yanke shine kawai takuma inda take ganin ya fimata shi addinin musulci batakura

 3. Musulmi Baya komawa wani addinin . Idan har ya tabbata chewa christace, to dama ta dade da fita a Musulunci tana kafurcinta. to chan dasu gada wai zomo yaji kidan farawta.

 4. Slm nidai haryanzu banji ta amsa da bakinta cewa takoma addinin cristaba. Kodai akwai inda tayi wani mgn mai kama da haka?

 5. Tabbas yahudawa sun rudi wannan yarinyan dama kuma akwai alaman batada tarbiya irinna addinin musulunci, shiyasa malamai ke cewa hana yin drammar hausa film shiyafi don shine sila ta lalacewar al umma. Allah ya shiryi Rahama sadau

 6. Shin kayan da take sakawa na addinin Kristanci ne? ko kuwa kuna son kuyi wa Kristanci batanci ne kuma… jaruman tana da daman yin addinin da take so mudin mulinci bai to mata, amma ku sani cewan Kristanci yafi mulinci darajanta zaman tsarki a kowace fanni na rayuwa. kuma irin halayan jaruman na sunyi nesa da Kristi Yesu! balle ma kuci ta zama krista don irin shigar da takeyi

  1. Amaganarka akwai gyara babu wani addini dayafi daraja dan adam kamar musulinci dan haka yakamata kasan mekake cewa

 7. ikon Allah!
  ta yi musulunci ko kiristanci,wannan a kanta ne.
  Amma ta sani cewa Wanda take bi wato turawa da ‘yan kudu,ko kadan ba za su daukaketa yanda ta ke tsammani ba,qarshe ma su saka mata qanjamau ta dawo gidansu ta na kashi a jikinta.

  1. Jahilci ba kyau, saboda day Allah Iya shegen da wadansun Ku Suna yin ta aboye bai fi nataba? Haba, mutum Sai ya rufe laifin SA ya dinga hango Na Wani, alhalin Idan an gan naku Har kurkuku Sai an kai Ku. Sannan kuna maganan cewa Ko ta koma Krista ne, Mai damuwan Ku da adinin da ta zabe was Kanta, is she a baby? Wanda yayi gaba ya riga yayi gaba, Ku je Ku nema was iyalen Ku abinci Ku bar Yar mutane ta huta.

  2. Talaka dai harwa yau jahiline ,don’t dai kawai bata da mulki a hanunta ,masu yin wanna kalaman ,suna ina lokacinda akayi auren Dan Buhari ? Wace irin kaya Amaryarsa ta saka ? Wanene yayi tsokaci a kai ? Haba jama. ,a ,Iowa ya binciki kansa tukuna ,

 8. Musulmai suna bani Mamaki gaskiya. Kuma Babu wadda a cikinsu zai gaya mini cewa haka addinin Kristiyanati ta koyar da Krista su Rika sa Kaya. Kuma fa Rahama ba a gidan Krista ta tashi ba. Don me zaku alakanta shigarta da addinin Kristanci? In muka ce duk musulmai Terrorist ne sai ku ji haushi. Don Allah ku Dena yiwa addinin Kristanci mummunar fahimta. Kristiyaniti Bata koyar da wani banzar shiga ba. In Kuma Kuna alaka da yanayin Yan kudu ne, toh ai wannan yanayinsu ne. Kuma addinin Kristanci Tana tir da shi.

 9. Toh jama,a Yan uwana maza da Mata muyi hakuri wannan dai magana haryanzu baku tabbatar ba CeCe kuce kawai ake Kai muyi hakuri da yada wannan abun domin bai zama gaskiya ba

  Allah yasadamu ta gane gaskiya ameen ya Allah

 10. Kamata yayi ace munga tafito ta fada da bakinta, Kafirta musulmi fah ba’abune mai sauki ba Dan Allah adinga kiyayewa. Ita kuma Allah Yasa ta daina ya shirya ta mudai musulmai kullun qaruwa mukeso a’addinin mu.

 11. Jahilci ba kyau, saboda day Allah Iya shegen da wadansun Ku Suna yin ta aboye bai fi nataba? Haba, mutum Sai ya rufe laifin SA ya dinga hango Na Wani, alhalin Idan an gan naku Har kurkuku Sai an kai Ku. Sannan kuna maganan cewa Ko ta koma Krista ne, Mai damuwan Ku da adinin da ta zabe was Kanta, is she a baby? Wanda yayi gaba ya riga yayi gaba, Ku je Ku nema was iyalen Ku abinci Ku bar Yar mutane ta huta.

 12. Kowa da kiwon da ya karbeshi, ban yi tsammani kayan sawa na da alaka da adinen nan guda uku ba, Krista, musulunci, da yahudanci….sai dai karamar sani cuta be sosai. Munga kayar da masu hannu da shuni suka Sanya wa yayansu mata, lokachin da za’a aurad dasu, ba sai mun kira suna ba. Don haka mu maida hankali ga masu sace Yara a makaranta da kisan gilla ga al’umma, mu bar barwar Allah ta yi abinda take so….akwai ranar gobe kiyama. Allah ya sa mu dace.

 13. Amma ya kamata mutane su daina yanke hukun ci da wuri haka, imma ta fita kantašŸ¤·idan ta xauna Kuma haka , Dan babu abunda xata karawa musulunci, tunda dai ba wani gudu mawa ta nasiya ko Kuma na tunatarwa take yiba , toh menene abun da muwa Kuma šŸ¤” nan

 14. Duniya ta isa kowa Riga da wando be Kuma ta zuba ta gani bakin Allah sanbarka ya yaqare balle na Allah tsine

 15. Kai duniya!!!
  Wai me yasa in baku zagi addinin kristanci ba, baku samin jin dada a rayuwarku! .ina da tambaya. Akon Krista ne? Classic Krista ne? Inta ma’amala dasu, shin su ba mutane bane? Meyasa kuna duba laifin wani kuna barin naku? me yasa kuna yi mata zato? Shin ganta da idonka a iklisiya nata ibadan?
  Mu kristoci an koya Mana yafewa, gafartawa duk wanda yayi Mana kasafi da kuma mu bar ramako Ubangi yayi, haka zalika sheri’a na Ubangi ne. Yesu be kadai zai dawo ya sharanta duniya.
  God your peace, love and direction I pray you gave us in nigeria. Amen

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button