Jarumar kannywood Nafisa Abdullahi ta cikin shirin, LABARINA, ta sami daukakar zama jakadiya a kamfanin Pepsi Naija

Shahararriyar jaruman fina-finan masana’antar kannywood wanda ta dauki lambobin yabo a cikin shirin nan mai dogon zango, LABARINA, wanda a cikin shirin ake kiranta da Sumayya wanto Nafisa Abdullahi, Allah ya kawo mata daukakar zama jakadiya a kamfanin Pepsi Naija.
Kamar yadda kuka sani Nafisa Abdullahi nata nada daga cikin manyan jaruman masana’antar kannywood wanda sun dade suna taka leda a kannywood, duba da yadda suke nuna kwarewar su a shirin fina-finan da suke bayyana.
Jaruma Nafisa Abdullahi ta bayyanawa al’ummar duniya cewa: Tana son ta sanar wa al’unma cewa ta sami wata yarjejeniya mai ban mamaki wanda ta zama jakadiya a kamfanin Pepsi Naija.
“Hey instafam, just wanna let y’all know that I just signed an amazing deal with @pepsi_naija and I’m really excited about this one! Say hello to the newest “PEPSI AMBASSADOR “…..
#pepsiambassador
#Pepsi”
Kamar yadda zakuga hotunan jarumar a wajan kamfanin Pepsi din inda take sanya hannu na yarjejeniyar zama jakadiyar tasu.
Ga hotunan domin ku kalla.