Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Jarumar Nollywood dake Kudancin Nageriya Halima Abubakar ta fadi magana akan jarumar Nageriya gaba daya wanda jama’a suka tofa albarkacin bakin su

kamar yadda kuka sani a kwai masana’antun shirya fina-finai guda biyu 2 a kasar Nageriya wato Kannywood da Nollywood, wanda sukan shirya fina-finai masu kawatarwa kama daga na turanci zuwan na hausa.

Advertising

Masana’antar kannywood masana’anta ce wacce ake shirya fina-finan hausa a cikin ta wanda ta kasance a Arewacin Nageriya, sabida yawancin al’ummar Arewa hausawa ne.

Nollywood kuma a Kudancin Nageriya suka fi shirya fina-finan su duba da yadda yarensu ba daya yake dana al’ummar Arewa ba, shiyasa zakuga kwata-kwata basa shirya fina-finan su da hausa.

Sai a wannan lokacin muka sami wani labari akan jarumar Kudancin Nageriya mai suna, Halima Abubakar inda take bayyana rashin saninta ga yawan jaruman kasar Nageriya gaba daya kama daga Nollywood har Kannywood.

Advertising

Inda jaruma Halima Abubakar take fadin cewa: ‘Yan fim a a Nageriya sunyi yawa, jarumar ta bayyana hakan ne a shafinta na sada zumunta Instagram kamar yadda LB suka ruwaito.

Sannan jarumar t akara da cewa: Batasan kashi tamanin 80% na ‘yan fim a Nageriya ba, wanda zancan nata tabbas yana kan hanya domin akwai jarumai masu yawa sosai a kasar Nageriya wanda ake shirin fina-finai da su.

Halima Abubakar ficacciyar jaruma ce a masana’antar shirya fina-finai dake Kudancin Nageriya wato Nollywood, jarumar ta bayyana hakan ne bisa rashin sanin da tayiwa jaruman kasar Nageriya gaba daya.

Idan kukayi duba da Arewacin Nageriya masana’antar kannywood ta samar da jarumai masu yawan gaske a cikin ta, wanda idan kun lura da kyau zakuga daga mazan har matan suna da yawa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button