Yanzu-Yanzu: Gaskiyar labari ya bayyana akan mutuwar jarumar kannywood Amal Umar
A wata bidiyo da muka muka samu daga wata tasha dake kan manhajar Youtube mai suna, Murna hausa Top Tv, sun wallafa gaskiyar al’amari akan labarin mutuwar jarumar masana’antar kannywood Amal Umar.
kamar yadda kuka saba da jin labarin shaci fadi wanda ake wallafawa akan jaruman kannywood, yanzu zakaji ance wani jaruma a kannywood ya rasu sai labarin ya gama karade kafafan sada zumunta daga baya kuma sai kaga jarumin ya bayyana a cikin bidiyo yana karyata labarin da aka wallafa a kan sa na cewa ya mutu.
Irin wadannan labaran na shaci fadi sun sha faruwa akan jaruman kannywood da dama kamar irin su, Rabiu Rikadawa, Jamila Umar Nagudu, Gadiza gabon, Daddy Shikima jarumin da yake sharafin sa a tanzu da dai sauran jarumai.
Yawan wallafa labaran karya akan jaruman na kannywood yakan janyowa masana’antar cece-kuce da kuma maganganu marasa dadi, wanda har a kwanakin baya masana’antar ta rasa zaman lafiya inda jama’a suka fara tunanin ko karshen masana’antar ne yazo duba da yadda rigingimu sukayi ta kaurewa a cikin masana’antar ta kannywood.
Sai a yau kuma muka sami wani faifai bidiyo daga manhajar Youtube wanda tashar, Murna hausa Top Tv ta wallafa, inda a cikin bidiyon zakuji gaskiyar al’amari akan mutuwar jarumar kannywood Amal Umar.
Ga bidiyon nan domin ku kalla.
Karanta wannan Labarin.
Karanta wannan Labarin.
Karanta wannan Labarin.