Jarumar kannywood Zainab Indomie gaskiyar al’amari akan abubuwa da suka faru a rayuwar ta
kamar yadda kuka sanin Zainab Indomie ficacciyar jaruma ce a masana’antar kannywood wanda ta dauki lambobin yabo a masana’antar, jaruman tajima ba’a ganin ta a cikin fina-finan kannywood inda tayi batan dabo.
Sai a wannan lokacin kuma jaruma tayi shira da ‘yan jarida inda take bayyana yadda rayuwarta ta kasance a lokacin data shiga harkar fina-finan kannywood.
Jarumar ta fara da cewa: Da farko sunana Zainab Abdullahi wanda kowa yafi sani na da Zainab Indomie, ni ‘yar asalin garin Abuja ce sannan kuma a can nake gudanar da rayuwa ta.
A garin Abuja nayi karatuna tun daga Pramary har Secondary sannan kuma nayi Diploma a jihar Kaduna, bayan na gama karatu kuma sai na shiga harkar fim wanda dama tun ina karama nake sha’awar kallon fina-finan hausa.
A duk lokacin da nake kallon fim din hausa ina kasancewa cikin nishadi da din dadi hakan yasa nake burin nima na shiga harkar ta fim, sai kuma Allah yayi ikon sa inda na sami damar shiga harkar sannan kuma na zama tauraruwa a masana’antar kannywood.
Kafin na sami damar shiga harkar fim na sha wahala sosai amma dana jore sai Allah ya taimakamin inda na sami damar haduwa da ficaccan jarumin masana’antar wato Ali nuhu.
Bayan mun hadu da shi sai ya fadawa iyayena maganar sannan suka amince sai suka gamka ni a hannun sa a matsayin sun bashi amana ta, shi kuma ya yarda daga nan ya fara sanya ni a cikin shirin fina-finan sa.
Bani da wani ubangida a masana’antar kannywood da yawuce Ali nuhu inda naje ganin ma yawuce ubangida a wajena sai dai uba sannan kuma dan uwa.
Shirin fim din dana fara bayyana a ciki wanda ya daukaka daraja ta sannan ya haskakani shine, Garinmu Da Zafi, wannan fim din shine wanda na nafi so a duk fina-finan dana yi.
Kalli bidiyon nan domin kaji cikekken bayani daga bakin jarumar.