Advertising
Advertising
Labarai

Kalli bidiyon wata budurwa mai suna Fauziyya Muhammad wanda ta zazzagi malamin addini akan ya fadi gaskiya kan auren su

A cikin wata bidiyo da muka samu munga yadda wani babban malami yake bawa maza shawara akan matan da yakamta su aura, sannan yake bayyana abubuwan da ya kamata suyi a lokacin da suka tashi yin aure.

Advertising

A bayanin da malamin yake yana fadin cewa, idan lokacin auran ka yazo kaga macen data burgeka kuma kana ganin ita ce ta kwanta maka a rai, to ko kaji mutane suna mata zargin cewa ita mazinaciya ce ko antaba lalata da ita to ya kamata ka bayyana mata cewa sai tayi jini sannan za’a daura muku aure.

Sannan kuma malamin ya kara da cewa, tunda har kana da niyyar auren ra zaka iya sanar da iyayanta cewa abarta tayi jini bayan ta gama sai a daura muku auren, babu zancen kunya ko kuma wani abu daban sabida hakan shine mafita domin gudun matsala.

Bayan wannan bidiyon malamin ta bayyana a lokacin da yake wa’azin sai wata matashiyqr budurwa mai suna Fauziyya Muhammad, wanda take amfani da wani suna na daban a manhajar TikTok inda ake kiranta da Feezy1234.

Advertising

Fauziyya Muhammad tayi martani akan wannan magana da malamin yayi sannan tayi zagi da wasu kalamai na daban ga malamin.

Amma daga baya Fauziyya Muhammad ta nemi afuwa akan wannan kalaman zagin da tayi, bayan jama’a sunyi mummunar fashimta ga kamalma nata.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

https://youtu.be/YDDusWDqa8Q

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button