Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Tirkashi: ‘Yan jarida sun sako jarumi Adam a zango a gaba kan alkawarin da yayi na daukar nauyin marayu 100

Zuwa ga Adam a zango ina aka kwana da marayunka na Zaiyar?.

Advertising

Wani bawan Allah mai suna malam Bashir yahuza malunfashi ya taso da wata magana data faru a shekarar data gabata, wanda maganar ta karade kafafan sada zumunta kan cewa jarumi Adam a zango ya dauki nauyin wasu marayu, inda ya kashe kudade har Naira Miliyan 47.

Kamar yadda jarumin ya bayyana a lokacin kan cewa ya dauki nauyin marayun akan kula dasu ta fannin ciyar dasu da shayar dasu da kuma ilimin su.

Sai dai tun wacan lokacin da jarumin yayi wannan alkawarin ba’a kara sanin ina aka kwana ba, shine wannan bawan Allah wato malam Bashir yahuza malunfashi ya taso da maganar domin sanin halin da ake ciki.

Advertising

Inda malam Bashir yahuza malunfashi ya fara da cewa: Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan kana lafiya, Allah sanya haka, Amin.

Bayan haka ba tare da bata lokaci ba na rubuta maka wannan sako ne da nufin jin inda aka kwana dangane da babban abin alkairin da kayi ikirarin ka aikata a bara (Oktoba 2020), inda ka sanar da al’umma cewa.

Ka fidda zunzurutun kudade har Naira miliyan 47 domin daukar nauyin wasu yara marayu sama da 100, a wata makaranta mai zaman kanta mai suna, Professor Ango Abdullahi Collefe.

Domin kuji cikekken labari akan sakon da aka turawa jarumi Adam a zango kan alkawarin da yayiwa yara marayu, sai ku kalli budiyon dake kasa.

https://youtu.be/ZIcDCPG3y-w

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button