Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Cikin kwana 3 da haska sabon fim din mu mai suna Fanan mun sami ribar Naira(1,245,500) cewar jaruma Mansurah Isah

Tsohuwar jarumar masana’antar kannywood wato Mansurah Isah ta wallafa wani sabon labari a shafin ta na sada zumunta Instagram akan sabon shirin fim din da suka haskaka mai suna Fanan.

Advertising

Mabsurah Isah dai ta kasance mata ga jarumin kannywood Sani musa danja, wanda a kwanan nan Mansurah Isah suka fitar da wani sabon shiri mai suna Fanan, wanda tun kafin bayyanar fin din wakar sa ta gama daukar hankulan jama’a.

Sai a yanzu kuma jarumar ta wallafa wanu dan gajeran labari a shafin ta na sada zumunta Instagram, inda take cewa.

Fin din Fanan ya bude da babban kasuwa a sabuwar sinimar nan (@Platinumcenimesng) fim din ya hada Naira Miliyan daya da dubu dari biyu da arba’in da biyar da dari biyar (1, 245, 500) a sinima daya rak, a ranar farko(1st Day)

Advertising

Tabbas fim din Fanan ya dau hazo alabashi a yanar gizo duba da yadda wakan fim din mai taken “Fanan” wacce mawaki mai zamani @Umarmshareef ya rera ra zama chartbuster song tun daga satin data fita.

Wanda babu tantama tana daya daga cikin jigon wannan nasara, FimMajer din sunyi kokari matuka wajan tallata fim din loko da sako wanda hakan fina-finai da waya suka rasa, shi kuwa fim din sinima sai da talla don hausawa dama sunce mai talla shike da riba.

Sannnan kuma jaruma Mansurah Isah ta wallafa wata bidiyo a shafin nasa akan wannan sabon fim din nasu mai suna Fanan, kamar yadda zakuga bidiyon a kasa.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button