Advertising
Advertising
Labarai

Subahanallah: wata budurwa ta tona asirin wasu samari da suka sace ta suke lalata da ita har tsawon kwana goma 12

A yanzun nan ne muka sami wani faifai bidiyo daga wata tasha mai suna, Rigar ‘Yanchi, dake kan manhajar Youtube, inda a cikin bidiyon muka ga wata mata tana bayyana mummunan abin da yafaru ga rayuwar ta.

Advertising

A cikin bidiyon zakuji yadda wata matashiyar budurwa take bada labarin akan wasu matasa da suka sace ta sannan kuma suka kaita wani gida suke lalata da ita, basu kyaleta ba har sai da tadauki tsawon kwana 12 a gidan.

A lokacin da ake shira da budurwar ta bayyana cewa, matasan basa bata abinci sannan kuma kullum sai sunyi lalata da ita, wanda har raba lokatun sukayi nayin lalata da budurwar, idan yau wani yayi lalata da ita gobe wani sai yayi.

Sannan kuma budurwar ta bayyana cewa, matasan su biyu 2 ne amma daga baya ta sami damar kunuta daga hannun su, a lokacin da tacika kwana goma sha biyu 12 a wajan su sai taji suna zance akan cewa an kama wani abokin su wanda suke harkar tare.

Advertising

Nan take kuwa suka fara yankewa shawarar barin garin inda har wani daga cikin su yake fadin inda zai nufa sabida baya so asirin sa ya tonu.

Haka budurwar ta cigaba da bayyana wannan abubuwan da suka faru ga rayuwar ta, kamar yadda zakuji cikekken bayanin daga bakin ta a cikin bidiyon da zaku gani a kasa.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button