Labaran Kannywood

Wani matashi ya aikewa da jarumar kannywood Hadiza Saima wasikar soyayya.

Tirkashi wani matashi dan asalin jihar kano ya aikewa da jarumar kannywood Hadizan Saima wasikar soyayya.

Wasikar da matashin mai suna Farouq Abdullahi Tukuntawa ya aikawa da jarumar a shafin sada zumunta na facebook ya nuna cewa matshin ya dade yana sonta. Ga wasikar da matashin ya rubuta zuwa ga jarumar.

WASIKA ZUWA GA HADIZAN SAIMA

Aminchi agareki…
Hajiya Hadiza hakika na Dade ina rokon Allah madaukakin Sarki ya nuna min kwatankwachin wannan rana kafin na koma gareshi.

Ranar da zan furta miki abun da ya Dade azuciya ta koda zaki dauki hakan a matsayin shirme, zan yi farinciki da hakan domin nasan nayiwa zuciya ta babban gata domin na fitar mata da ciwon da ya Dade yana dawainiya da ita.

Hakika Son ki ya shiga zuciyata ya ratsa jini na da tsokata, Yayi gunduwa gunduwa da hanjina ya fatattaka koda da tumbina ya ragargaza kayan cikina.

Ya ratsasa hanta da qasusuwa na da 6argo na, Ki agaza min ki cechi rayuwata ki tsamo ni daga kogin soyayyarki Dana fada.

Bana iya chin abinchi bana iya bacchi koda na kwanta hoton kyakkyawar fuskarki ne kawai yake min yawo a idona.

I love you with All my heart baby na
Idan na sameki na gama cika burina
Rashin ki dai-dai yake da tarwatsewar dukkan farin cikina.

Ki huta lafiya daga masoyinki har abada
Farouk Abdullahi Tukuntawa.

Hadiza Saima
Farouq Abdullahi Tukuntawa

Matashin ya aje number waya sa domin idan taci karo da sakon ta kirashi don jin matsayin soyayyar sa. Ba wannane karo na farko da Samari suke neman Jaruman kannywood da aure ba musamman iyaye a masana’antar.

8 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button