Yanzu-Yanzu: Jarumi Lawan Ahmad yayi Mushimmiyar sana’ar akan shirin IZZAR SO EPISODE 65
Kamar yadda kuka sani shirin IZZAR SO shiri ne wanda yake zuwa muku a duk sati wanda tashar BAKORI TV dake kan manhajar Youtube take haskaka musu shirin.
Idan bazaku manta ba wancan satin da yagata ba’a gaskaka shirin na IZZAR SO ba, inda jama’a da dama masu a kallon shirin suke dakon wannan satin domin kallon shirin.
Sai kuma a yanzu muka sami wata sanarwa daga shafin sada zumuntar Instagram na jarumin shirin fim din na IZZAR SO wato Lawan Ahmad, inda yake sanarwar kamar haka.
A yau babu zango na 65 sai ranar 7 ga watan Nuwamba idan Allah ya kaimu, jarumin yana nuna cewa a yanzu haka ana daukar shirin fim din na IZZAR SO.
Sannan kuma sai muka sake cin karo da wani hoton jarumar cikin shirin na IZZAR SO a shafin nasa wato Aisha Najamu, inda mukaga wata wallafar rubutu a kasan hoton nata wanda yayi dai-dai da irin rubutun da jarumi Lawan Ahmad ya wallafa akan shirin na IZZAR SO.
Inda muka sake tabbatar da bazasu haskaka wannan shirin nasu ba na IZZAR SI EPISODE 65 sai zuwa ranar 7 ga watan Nuwamba, kamar yadda suka sanar.