Innalillahi: Yanzu aka kama wani karamin yaro da yake sace kananan yara a buhu yana kaisu wani waje
Wannan abin takaicin da mai yayi kama, jami’an ‘yan sandan jihar Kano sunyi nasarar kama wani maramin yaro wanda yake sace kananan yara, sannan kuma yaron ya fara sana’ar jari bola be kafin ya fara satar yaran.
Abubuwan takaici suna yawan faruwa a wannan kasar tamu ta Nageriya abubuwan sunyi yawa da bazasu lissafu ba, kuna hakan ya samo asali ne daga jama’ar kasar inda suke bada gudunmawar su wajan lalacewar kasar.
Wannan karamin yaron da yake aikata wannan mummunan aikin na sace kananan yara babu zancen kyakkyawar rayuwa a tattare da shi, domin ba tabbacin yaron yaron yana karatu balle ayi zaton zai iya zama mutum na gari nan gaba.
A cikin bidiyon zakuga jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan nihar Kano wato, DSP Avdullahi Kiyawa, yana magana da wannan karamin yaron da yake sace kananan yara.
Kamar yadda kuka sani wannan kasar tamu ta Nageriya tana fama da matsalolin da suke taddabar al’umma mazauna cikin ta, wanda har ma abin yake nema yayi yawa.
A wannan zamani da muke ciki sace-sacen mutane a kasar Nageriya ya zama ruwan dare ko mutum yana gida a kwance ba abin mamaki bane idan aka ce an sace shi, domin ko kana gida baka gagara a sace ka ba.
Sannan kuma ga matsalar ta’addancin da kasar Nageriya take fama da ita wanda har yanzu an kasa gano bakin zaren wajan kawo karshen ta’addancin.
Yanzu dai a cikin bidiyon zakuga yadda jamu’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano,DSP Abdullahi haruna kiyawa yana yiwa yaron tambayoyi akan wannan satar kananan yaran da take.
Ga bidiyon nan a kasa domim ku kalla.