Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Mansurah Isah tace sabon fim din ta mai suna Fanan ya kafa tarihi a kannywood dalilin kudin data samu Naira Miliyan 20

Kamar yadda kuka sani a shekaran jiya ne tsohuwar jarumar masana’antar kannywood Mansurah Isah ta fara haska fim din ta mai suna fanan, a sabuwar cenimar Platinum dake Zaria Road a jihar Kano.

Advertising

Inda masoyanta da kuma abokan sana’arta suka galarci wajan haska fim din nata mai suna Fanan, sannan kuma fim din yaja hankulan jama’a da dama wanda sunyi mamakin daukakar da fim din ya samu.

Akwai wani kamfani mai suna kannywodd box iffice wanda yake bayyana kudaden a duk wani fim yake samu a cenima, kamfanin ya bayyana yawan kudin da aka samu a wannan sabin fim din wato Fanan.

Inda Mansurah Isah ta sami kudade masu yawa kimanin Naira miliyan daya da dubu dari biyu da arba’in da biyar da bari biyar (N1,245,500), a ranar farko da aka fara haska fim din nata mai suna Fanan.

Advertising

Sannan kuma tsohuwar jaruma Mansurah Isah ta bayyana kudin data samu kafin ayi wannan lissafi, inda tace ta sami kudade kimanin N8,000,000.

Ta sami wadannan kudaden ne a wasu alluna na daban da aka haskaka wannan shirin nata wanda a lokacin data sami wannan kudade sai data bayyana farin cikin ta.

A yanzu haka dai Mansurah Isah a hada kudade kimanin sama da N9,000,000 a lokacin data haskaka shirin nata mai suna Fanan.

Bayan ga haka kuma ta bayyana cewa: Ban da wasu kamfanunuwa na daban data wasu talla wanda a kalla fim din nata zai iya hada mata kudade kimanin Naira miliyan ashirin N20M.

Sannan kuma ta bayyanan muenar ta akan kudaden data samu akan wannan fim din nata mai suna Fanan, har ma take fadin cewa fim din nata Fanan ya kafa tarihi masana’antar kannywood.

Ku kalli bidiyon dake kasa domin kuji cikekken labari.

Advertising

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button