Subahanallah: An kama mutumin da yake yiwa yara mata fyade amma ya dangana abin da cewa matarsa ce sila
A cikin wani faifai bidiyo da muka samu daga tashar Rigar ‘Yanchi dake kan manhajar Youtube, an kama wani mutumi wanda yake yiwa yara mata fyade.
A cikin bidiyon anji ta bakin mutumin yadda yake bayyana dalilin da yasa yake aikata wannan mummunan barnar ta yiwa ‘yan mata fyade.
Inda mutumin yake cewa, sanadiyar rashin kulawar matar sa shine ya jefa shi cikin mummunan aiki, domin bata bashi kulawa yadda ya kamata.
Mutumin ya jima yana aikata wannan barnar wanda dama hausawa suna cewa rana dubu ta barawo rana daya ta mai kaya, an kama shi ne bayan ya aikata fyade ga wata karamar yarinya.
Bayan an kama shi ana masa tambayoyi akan abin da yake aikatawa sai yake bayyana cewa, duk abin dake faruwa ta silar matar sa ne domin tana tafiya yawon karuwanci shi kuma ta kyale shi bata bashi lokacin sa.
Mutumin yaci gaba da cewa: Tun daga wannan lokacin da matar sa ta fara tafiya yawon karuwancin shima ya soma yiwa yasara kanana fyade.
Asirin mutumin ya tonu ne bayan kama shi da akayi da wata karamar yarinya wanda duka-duka bata fi shekaru goma 10 ba yana lalata mata rayuwar ta.
Ga bidiyon nan domin ku kalla kuji cikekken bayani daga bakin mutumin.