Wasu daga cikin jaruman kannywood mata sun tonawa abokiyar su asiri akan bin maza da bokaye tare da yiwa darakta asiri
Kamar yadda kuka sani kannywood masana’anta ce wanda ta tara jarumai maza da mata da ake shirin fim da su, wanda a yanzu kuma masana’antar ta karo sabbin harumai wanda ake shirin fim mai dogon zango dasu.
Sai a yanzu kuma muka sami wani saban labarin akan jarumar masana’antar kannywood mata yadda suka bayyana wasu abubuwa ga abokiyar aikin su, wanda hakan bai dace ba duba da yadda sana’ar su daya.
Jaruman sun bayyana a cikin wata bidiyon da suka wallafa ta a manhahar TikTok suna tonawa abokiyar tasu asirida fadin abubuwan da zasu iya janyowa kannywood din cece-kuce, kamar yadda aka saba yi.
Amma wadannan jaruman da suka aikata hakan sababbi ne a masana’antar ta kannywood wanda ake kiran su da jaruman shiri mai dogon zango wato Series.
Jaruman sun yiwa wata abokiyar su tofin alatsine a manhajar TikTok inda suka jero kusan su biyar suna la’antar abokiyar tasu ta kuma fadin aibunta kala-kala, inda suke cewa abokiyar tasu tana bin Boka da biye-biyen maza tare da yiwa tare da yiwa Darakta asiri.
Sai dai kuma duk wannan la’anta da zagin da suke yiwa abokiyar tasu basu kama sunanta ba kamar yadda suke cewa ai tasan kanta, amma wannan mummunan lafazi da suke akab kawar tasu zai iya barin baya da kura.
Abin da sukayi tamkar suna neman tonawa kansu asiri ne duba da gaba dayan su a masana’antar kannywood din suke amma suke fadin wani abu wanda ake zagin wata jarumar kannywood da aikata shi.
Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji abubuwan da jaruman suke fadawa abokiyar tasu.
Ga bidiyon nan domin ku kalla.