Wata mata ta bayyana yadda rayuwar hausawa take kasancewa a kasar Saudiyya inda itama aka nemi yin lalata da ita
Yanzu yanzu muka sami wata bidiyo daga tashar Al’-Fusqan wal huda Tv dake kan manhajar Youtube, inda a cikin bidiyon zakuji yadda akayi shira da wata mata akan hausawa mazauna kasar Saudiyya.
kamar yadda malamin ya fara da cewa: a halin da al’ummar hausawa mazauna kasar saudiyya suke ciki ansha kace-nace tare da dayin maganganu da dama da suka janyo ran wasu ma ya baci.
Cikin wadanda rayukan nasu ya baci suma mazauna kasar saudiyyar ne, kamar yadda kuka sani akwai hausawan dake tafiya kasar saudiya domin yin wanu abu daban wanda ba na samin laba bane.
Kasar saudiyya dai kasace mai tsarki wanda ake zuwa domin a gudanar da wasu aiyukan samin lada da kuma neman gafara wajan Allah, amma wasu sukan niki gari suje wannan kasar mai tsarki domin aikata abin da ba alkairi bane.
Ita ma wannan matar da ake shirar da ita tana daya daga cikim mazauna kasar saudiyya kuma tana da hali mai kyau inda har ma ta bada labarin rayuwar da tayi a kasar saudiyya kamar yadda zakuji a cikin bidiyon.
Matar ta bada tashirin rayuwar da tayi a gidan larabawa wanda take musu aiki, a cikin bayanin nata take cewa wani mahaifi tare da dansa a kullum sai sun nemeta da yin lalata amma sai taki.
Sannan kuma tace, da farko mahaifin ne ya fara nemanta fa yin lalatar amma taki amincewa, daga nan kuma sai dansa ya fara nemanta amma daga karshe mahaifin yaron sai ya nemi auren ta inda ya bayyana mata dukiyar sa a nan ma sai taki.
Bayan taki amincewa sai yayi mata dukan tsiya da bin kwasar shara, bayan ya gama dukan nata sannan ya kadota waje inda duk kayan jikinta basa rufe mata surar jikinta.
Sannan kuma matar ta bayyana abubuwa da dama akan hausawa mazauna kasar Saudiyya inda duk zakuji bayanin nata a cikin bidiyon.
Ga bidiyon nan domin ku kalla kuji cikekken bayani daga bakin matar.